:

Daga Salaiman Bin Surad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ina zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali wasu mutane biyu suna zage-zage, ɗayansu fuskarsa ta yi jā, jijiyoyinsa sun buɗe, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi" sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan", sai ya ce: Shin ni ina da hauka ne?

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

wasu mutane biyu sun yi zage-zage a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali fuskar ɗayansu ta yi jā, jijiyoyinsa da suka kewaye wuyansa sun kunbura. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na san kalmar da wannan mai fushin zai faɗeta da fushin ya tafi daga gare shi, da zai ce: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa. Sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan. Sai ya ce: Shin ni mahaukaci ne? ya yi zatan cewa ba mai neman tsari daga Shaiɗan sai wanda yake da hauka.

فوائد الحديث

Kwaɗayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan shiryarwa da fadakarwa a yayin samuwar sababinsa.

Fushi daga Shaiɗan ne.

Umarni da neman tsarin Allah daga Shaɗan abin jefewa a yayin fushi, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Idan fuzga daga Shaiɗan ta fuzgeka to ka nemi tsarin Allah..} Aya.

Gargaɗi akan zagi da abinda ke kama da shi na tsinuwa, da kuma nisanta daga garesu; domin su suna kaiwa zuwa ɓarna tsakanin mutane.

Kawo nasiha ga wanda bai ji ta ba dan ya anfana da abinda ke cikinta.

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga fushi; domin cewa shi yana kaiwa zuwa sharri da rashin tinani, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance ba ya fushi sai dai idan an keta alfarmar Allah - Maɗaukakin sarki -, shi ne fushi abin yabo.

AlNawawi ya faɗa akan faɗinsa: "Shin kana ganin ni ina da hauka ne": Zai yiwu cewa wannan mai maganar ya kasance yana daga munafukai, ko daga larabawan ƙauye masu wauta.

التصنيفات

Munanan Halaye, Zikiri domin wasu Abubuwa da suka bujuro