Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne

Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne

Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yace: "Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sanar damu cewa tsaftace hakora da itaciyar urak da makamancinta yana tsaftace baki daga datti da wari wadanda suke abin ki. Kuma cewa shi yana daga sabubban yardar Allah ga bawa; domin cewa a cikinsa akwai biyayya ga Allah da amsa umarninSa, da kuma abinda ke cikinsa na tsaftar da Allah - Madaukakin sarki - yake son ta.

فوائد الحديث

Falalar asiwaki, da kwadaitarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga al'ummarsa da yawaitawa hakan.

Abinda yafi ga asiwaki shi ne yin amfani da itacan urak (kirya), yin amfani da makilin da burush yana tsayawa a madadinta.

التصنيفات

Sunnonin Fixra