Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci

Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce akan minbari, kuma sai ya ambaci sadaka, da kamewa, da kuma roƙo: «‌Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci, hannu maɗaukaki: Shi ne mai ciyarwa (mai bayarwa) maƙasƙanci kuma: Shi ne mai roƙo».

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambata alahali yana huɗubar akan sadaka da kamewa daga roƙo akan minbari; sannan ya ce: Hannau maɗaukaki mai ciyarwa mai bayarwa shi ne nafi alheri kuma mafi soyuwa a wurin Allah daga hannu maƙasƙanci mai roƙo.

فوائد الحديث

A cikinsa akwai falalar bayarwa da kuma ciyarwa a hanyoyin alheri da kuma zargin roƙo.

A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan kamewa daga roƙo da kuma wadatuwa daga mutane, da kwaɗaitarwa akan kyawawan al'amura, da barin komabayansu, Allah Yana son kyawawan al'amura.

Hannaye guda huɗu ne, su a falala kamar yadda yake tafe ne: Maɗaukakinsu mai ciyarwa, sannan mai kamewa daga karɓa, sannan mai karɓa ba tare da roƙo ba, sannan komkabayansu shi ne mai roƙo.

التصنيفات

Sadakar Taxawwu'i, Ciyarwa