إعدادات العرض
Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur
Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी සිංහල ئۇيغۇرچە Português Kurdî Русский Tiếng Việt Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતીالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan sahur shi ne cin (abin ci) a ƙarshen dare dan yin tanadi ga azimi; domin cewa a cikinsa akwai (albarka) alheri mai yawa na lada da sakamako, da tashi a ƙarshen dare dan addu'a, da ƙarfafuwa akan azimi, da nishaɗuwa gare shi, da kuma sauƙaƙa wahalarsa.فوائد الحديث
An so sahur da riko umarnin shari'a da aikata shi.
Ibnu Hajar ya ce a cikn Fathul Bari: Albarka a cikin sahur tana samuwa ne ta ɓangarori masu yawa, su ne bin sunna, da saɓawa Ahlul kitabi, da ƙarfafuwa da shi akan ibada, da ƙari a cikin nishaɗi, da tunkuɗe munanan ɗabi'u wanda yunwa take taso shi, da kawo sababin sadaka ga wanda yake roƙo a wannan lokacin ko yake haɗuwa da shi akan cin abin ci, da sabbaba zikiri da addu'a a lokacin ana fatan amsawa, da riskar niyyar azimi ga wanda ya rafkana daga gareta kafin ya yi bacci.
Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da hikima; dan ƙirji ya buɗe da shi, kuma a san matsayin shari'a da shi.
Ibnu Hajar ya ce: Sahur yana samuwa ne da mafi ƙarancin abinda mutum yake samunsa na abin ci da abin sha.
التصنيفات
Sunnonin Azumi