Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta

Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta

Daga Abu Ubaid, 'yantaccen Ibnu Azhar, ya ce: Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani game da azimin ranar idin ƙaramar sallah da idin babbar sallah; amma idin ƙaramar sallah to ranar buɗa baki ce daga azimin watan Ramadan, amma ranar idin babbar sallah to ranar ci ce daga abubuwan layya.

فوائد الحديث

Haramcin azimin ranakun idin ƙaramar sallah da babba da kwanukan Tashriƙ; domin cewa su masu bi ne ga ranar babbar sallah sai dai ga wanda bai samu hadaya ba to azimin kwanukan tashriƙ ya halatta gare shi.

Ibnu Hajar ya ce: An ce: Fa'idar siffanta ranaku biyun dan nuni ga illa a wajabcin cin abinci a cikinsu, shi ne rabewa daga azimi, da bayyanar cikarsa shi kaɗai da karya azimin abinda ke bayansa, ɗayan kuma saboda yanka wanda ake neman kusanci da yankansa dan a ci daga gare shi.

An so ga mai huɗuba (liman) a cikin huɗubarsa ya tinatar da abinda yake rataye da lokacinsa na hukunce-hukunce kuma ya kintaci munasabobi.

Halaccin ci daga abin yanka.

التصنيفات

Abunda aka Haramtawa Mai Azumi