إعدادات العرض
Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama
Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහල Kiswahili Tiếng Việt অসমীয়া ગુજરાતી Nederlands አማርኛالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sakamakon musulmi a wurin Allah yana daga jinsin abinda musulmi yake aikata shi tare da musulmai; wanda ya yaye ya gusar ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki da tsanani daga baƙƙan cikin duniya, Allah Zai yi masa sakayya da cewa Zai Yaye masa wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin ranar alƙiyama. Wanda ya yalwatawa wanda ke ciki matsi ya kuma sawwaƙa masa ya gusar da matsinsa, Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira. Wanda ya suturta wani musulmi kamar idan ya tsinkaya daga gare shi akan abinda bayyanar da shi ba ya kamata na tuntuɓe da kurakurai, Allah Zai suturta shi a duniya da lahira. Allah Yana kasancewa Mai taimako ga bawanSa, muddin dai bawan ya kasance mai tafiya ne akan taimakon ɗan uwansa a maslahohinsa na Addini da duniya, taimako yana kasancewa ne da addu'a da jiki da dukiya da kuma wanin hakan. Wanda ya yi tafiya zuwa tabbatar da wani ilimi na shari'a, yana mai nufin fuskar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi; to Allah Zai sawwaƙa masa hanya zuwa aljanna da shi. Wasu mutane ba su taru ba a wani ɗaki daga ɗakunan Allah, suna karanta littafin Allah kuma suna mudarasarsa a tsakaninsu, sai nutsuwa ta saukar musu, rahamar Allah ta gamesu ta lulluɓesu, kuma mala'iku sun kewayesu, Allah Ya yi yabo a garesu a cikin makusantan dake wajenSa, kuma ambatan Allah ga bawa a cikin jama'a maɗaukaka ya isa ɗaukaka. Wanda aikinsa ya kasance tauyayye ne, Ba zai riskar da shi da darajar ma'abota ayyuka ba, to yana kamata kada ya dogara akan ɗaukakar nasaba da falalar iyaye, ya taƙaita a cikin aiki.فوائد الحديث
Ibnu Daƙiƙul Eid ya ce: Wannan hadisi ne mai girma, mai tattarowa ne ga nau’ukan ilimummuka da ƙa'idoji da ladubba, a cikinsa a kwai falalar biyan buƙatun musulmai da anfanar da su da abinda ya sawwaƙa, na ilimi, ko dukiya, ko taimako, ko nuni da wata maslaha, ko nasiha, ko wanin haka.
Kwaɗaitarwa a cikin yalwatawa wanda ke cikin matsi.
Kwaɗaitarwa akan taimakon bawa musulmi, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana taimakon mai taimako gwargwadan taimakonsa ga ɗan uwansa.
Daga suturta musulmi: Rashin bibiyar al'aurarsa, haƙiƙa an ruwaito daga sashin magabata ya ce: Na riski wasu mutane basu da wasu aibuka, sai suka ambaci aibukan mutane, sai mutane suka ambata musu aibuka, kuma na riski wasu mutane sun kasance suna da aibuka, sai suka kame daga aibukan mutane, sai aka manta da aibukansu.
Barin munkari da rashin canja shi bai zama daga lazimtar suturta mutane ba, domin in ya canja ya suturta, wannan a cikin haƙƙin wanda ba'asan shi da ɓarna ba da kuma zarcewa a cikin shisshigi ba, wanda aka san shi da hakan to shi ba'a son suturta shi, kai za'a kai al'amarinsa zuwa ga hukuma, idan bai ji tsoron ɓarna ba daga hakan; hakan domin suturta shi zai ruɗar da shi akan ɓarnar, kuma zai sa shi ƙarfin hali akan cutar da bayin Allah, kuma zai sa waninsa ma ƙarfin hali daga ma'abota sharri da tsaurin kai.
Kwaɗaitarwa akan neman ilimi da karatun alƙur'ani da mudararsa.
AlNawawi ya ce: A cikin wannan akwai dalilin taruwa akan karatun alƙur'ani a cikin masallatai... an riskar da masallaci a tabbatar da wannan falalar, taruwa a cikin wata makaranta ko zaman dako da makancin su in Allah - Maɗaukakin sarki - Ya so.
Sakayya kawai Allah Ya jeranta ne akan ayyuka ba'a kan nasabobi ba.
التصنيفات
Falalar Ilimi