Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi- Ba ruwan shi da mace mai yin kukakan kera, ko mai aske kanta, ko mai kyakketa tufafinta in wani abu marar dadi ya faru

Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi- Ba ruwan shi da mace mai yin kukakan kera, ko mai aske kanta, ko mai kyakketa tufafinta in wani abu marar dadi ya faru

Daga Abdullahi Dan Kais Allah ya yarda da shi: "Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi-Ba ruwan shi da mace mai ihu da kururuwa idan wata masifa ta afku,hakanan mace mai aske kanta,hakanan mace mai yayyaga tufafi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Abin da Allah ya karba ko ya bayar duka nashi ne,acikin kasancewar haka akwai hikima da shiryarwa, duk wanda ya bijirewa hakan kamar ya bijirewa kaddarar Allah ne wanda shi ne daidai kuma shi ne adalci.Don haka Annabi-tsira da aminci su tabbata a gare shi-ya fadi cewar duk wanda ya fusata yayi raki to,ba a kan tafarkinsa yake ba, ya koma hanyar masu yin raki idan sharri ya same su,don kuwa suna damfare da wannan duniyar,ba su kwadayin lada da yarda a wajen Allah game da masifar da ta same su,to shi ba ruwansa da duk wanda imaninsa ya raunana lokacin faruwar wata masifa har ta kai su ga fusata a zuci ko a bayyane,ta hanyar ihu da kururuwa da kiran an shiga uku,ko tsittsinke gashi,da yaga tufafi,don farfado da al'adar jahiliyya.Masoyan Allah kadai sune masu mika lamarinsu ga Allah lokacin faruwar masifa,kuma suce {Lallai daga Allah muke kuma gare shi muke komawa.Wadannan suna samun salati daga ubangijinsu da wata irin rahama kuma sune shiryayyu}

التصنيفات

Mas’alolin Hukuncin Allah da Kaddara Musulunci, Mutuwa da Hukunce Hukuncenta