Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa

Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa

Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa", kuma cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa daga maɓungura ƙasa, sai ya ji wari daga gareta, sai ya yi tambaya sai aka ba shi labarin abinda ke cikinta na maɓungura ƙasa, sai ya ce ku kusantar da ita ga wani daga sahabbaina wanda ke tare da shi, lokacin da ya ganta sai ya ƙyamaci cinta, ya ce: "Ka ci domin cewa ni ina ganawa da wanda ba ka ganawa (da shi)".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya ci tafarnuwa ko albasa zuwa masallaci, dan kada ya cutar da 'yan uwansa daga waɗanda suka halarci sallar jam’i da warinsu, shi hanine na tsarkakewa daga zuwa masallaci, ba dan an hana cinsu ba: domin cewa su suna daga abubuwan da aka halatta, haƙiƙa an zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa, lokacin da ya shaƙi wari a cikinta kuma aka ba shi labarin abinda ke cikinta sai ya hanu daga cinta ya kuma kusantar da ita ga wani daga sahabbansa dan ya ci daga gareta, sai ya kyamaci ci dan koyi da shi, lokacin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gan shi ya ce: Ka ci; domin cewa ni ina ganawa da Mala’iku idan sun zo da wahayi. kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'iku suna cutuwa daga warin da ake ƙi, kamar yadda mutane suke cutuwa daga gare shi.

فوائد الحديث

Hanin zuwa masallaci ga wanda ya ci tafarnuwa, ko albasa, ko algarif.

Ana riskar da waɗannan abubuwan, dukkan abinda yake da warin da masallata suke cutuwa daga gare shi, kamar warin taba da wiwi da makancin hakan.

Illar hanin “wari”, idan ya gushe da yawan dafuwa ko wanin hakan; to karhancin ya gushe.

Karhancin cin waɗannan abubuwan ga wanda zuwa sallah a masallaci ya wajaba akansa; dan kada jam'i ya wuce shi a cikin masallaci, muddin dai bai ci ba dan dabara akan kin halarta, to (cin) ya haramta.

Hanuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga cin tafarnuwa da makancinsa, badan haramcinsa ba ne, kawai dan ganawarsa ne da (mala'ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -.

Kyakkyawan koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da bayanin sababinsa; dan wanda ake magana ya nutsu da sanin hikimar.

Alkali ya ce: Malamai sun ƙiyasta wanin masallaci akan wuraren haɗuwa dan yin sallah, kamar wurin sallar idi da jana'iza da makancinsu daga wuraren taruwa dan yin ibadu, haka nan wuraren taruwa na ilimi da zikiri da walimomi da makancinsu, ba za'a riskar da kasuwanni da wasunsu da su ba.

Malamai sun ce: A cikin wannan hadisin akwai dalili akan hana cin tafarnuwa da makamancinta daga shiga masallaci - koda ya kasance ba kowa - domin shi guri ne na mala'iku, kuma saboda gamewar hadisan.

التصنيفات

Falalar Sallah cikin jama’a da Hukunce Hukuncenta