إعدادات العرض
Cewa Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin baƙin ciki: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mai girma kuma Mai haƙuri, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin al'arshi mai girma, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah,…
Cewa Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin baƙin ciki: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mai girma kuma Mai haƙuri, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin al'arshi mai girma, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai, Ubangijin ƙasa, kuma Ubangijin al'arshi mai girma
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - Cewa Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin baƙin ciki: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mai girma kuma Mai haƙuri, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin al'arshi mai girma, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai, Ubangijin ƙasa, kuma Ubangijin al'arshi mai girma».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी සිංහල Kurdî Português Kiswahili অসমীয়া Tiếng Việt ગુજરાતી Nederlands አማርኛ മലയാളം Română ไทย Magyarالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin tsananin baƙin ciki da takaici gareshi: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Mai girman" daraja, mai girman sha'ani, a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, "Mai haƙuri" wanda ba Ya gaggauto da uƙuba ga mai saɓo kai Yana jinkirtata, kuma Zai iya yi masa afuwa tare da iko akansa, Shi ne Mai iko - tsarki ya tabbatar maSa akan kowane abu. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi Mai girma. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da ƙasa" kuma Mahaliccin sammai da ƙasa, kuma Mahaliccin kowane abu a cikinsu kuma Mamallakinsa kuma Mai gyara shi , kuma Mai tasarrufi a cikinsa yanda ya so, "Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi mai girma.فوائد الحديث
Wajabcin gaggawar komawa zuwa ga Allah da addu'a a lokacin saukar musibu da baƙƙan ciki.
Anso addu'a da wannan zikirin a lokacin baƙin ciki.
Al'arshin al-Rahman wanda Ya daidaita akansa - Maɗaukaki - shi ne mafi ɗaukakar ababen halitta kuma mafi girmansu, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta shi da cewa shi mai girma ne.
An keɓanci sammai da ƙasa da ambato; domin cewa sune mafi girman ababen halitta waɗanda ake gani.
AlƊaibi ya ce: Ya fara da wannan yabon ne da ambato dan ya dace da yaye baƙin ciki; domin cewa shi ne mahukuntar tarbiyya, kuma acikinsa akwai Hailala wacce ta ƙunshi tauhidi wanda shi ne asalin tsarkake-tsarkake masu girma, da girman da yake nuni akan cikar iko, da haƙuri wanda yake nuni akan ilimi, dan jahili ba'a tinanin haƙuri ko kyauta daga gare shi , kuma sune asalin siffofin girmamawa.