Manzon Allah ya kasance yana yawan fada a cikin ruku'unsa da sujjadarsa: tsarki ya tabbatar maka ya Ubangijina da godiyarka, ka gafarta min.

Manzon Allah ya kasance yana yawan fada a cikin ruku'unsa da sujjadarsa: tsarki ya tabbatar maka ya Ubangijina da godiyarka, ka gafarta min.

Daga Aisha Allah ya yarda da ita tace: "Manzo -tsira da amincin Amincin Allah su tabbata a gare shi- bai taba yin salla bai fadi: " Subhanakallahumma Rabbana wa bihamdika, Allahummagfirli". A wani lafazin:"Manzon Allah ya kasance yana yawan fada a cikin ruku'unsa da sujjadarsa: tsarki ya tabbatar maka ya Ubangijina da godiyarka, ka gafarta min."

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Aisha Allah ya yarda da ita ta ambata a cikin wannan hadisin cewa Allah Madaukaki yayin da ya saukarwa Annabi tsira da amincin Allah suratun Nasr, kuma yaga alamar nasarar tare da bude Makka, sai yayi gaggawar bin umarnin Allah Madaukaki,sai ya kasance mafi yawan abin da yake fada shi ne: [tsarki ya tabbatar maka da godiyarka ya Ubangiji na ka gafarta min]. wadannan kalmomi, sun tattare tsarkake Allah Madaukaki daga dukkan tawaya, tare da ambaton godiyarsa, kuma suka kare da neman gafararsa tsarki ya tabbatar masa.bai sallaci wata sallar farilla ko ta nafila ba face sai ya fadi wadannan kalmomin a ruku'u ko asujjada.saukar wannan sura alamar kusantowar ajalin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

التصنيفات

Zikirin Sallah