إعدادات العرض
Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa
Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa
Daga Sahlu ɗan Mu'azu ɗan Anas daga babansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa".
[Hasan ne]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහල አማርኛ অসমীয়া Kiswahili Tagalog Tiếng Việt ગુજરાતી Nederlands پښتو नेपाली മലയാളം Svenska ไทย Кыргызча Română Malagasyالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya ci wani abinci da ya godewa Allah, babu wani iko gareni a samun abinci, ko a cinsa sai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma taimakonSa, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi wa wanda ya faɗi hakan bushara da cewa shi ya cancanci gafarar Allah gare shi a abinda ya shuɗe daga zunubansa ƙananu.فوائد الحديث
An so godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a ƙarshen cin abin ci.
Bayanin girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa, inda Ya azirtasu kuma Ya sawwaƙa musu sabubban arziƙi , kuma Ya sanya kankare munanan ayyuka a cikin hakan.
Al'amuran bayi gabaɗayansu daga Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, ba da dabararsu ko ƙarfinsu ba, kuma bawa abin umarta ne da aikata sabubba.