Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama

Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta cancanci amsawa, to ku roƙi Allah a cikinsa.

فوائد الحديث

Falalar wannan lokacin dan yin addu'a.

Idan mai yin addu'a ya siffantu da ladubban addu'a, kuma ya nufi gurarenta da lokutanta masu falala, kuma ya nisanta daga saɓon Allah, Ya tsare kansa daga afkawa a cikin shubuhohi da kokwanto, kuma ya kyautatawa Allah zato: To shi ya cancanci a amsa masa da izinin Allah.

Al-Manawi ya ce game da amsa addu'a: Wato: Bayan tara sharuɗɗan addu'a da rukunanta da ladubbanta, idan wani abu ya saɓa daga garesu to kada ya zargi kowa sai kansa.

Amsa addu'a: Kodai a gaggauto masa da abinda ya roka, ko a kawar masa da sharri kwatankwacin sa, ko a ajiye masa ita a lahira; hakan gwargwadan hikimar Allah da rahamarSa.

التصنيفات

Sababan Amsa Addu’a da kuma abubuwan da suke hana su