Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira

Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwami da lafiya a Addini na da duniya ta da iyalaina da dukiyata, ya Allah Ka suturta al'aurata - ko: al'aurorina Ka amintar da tsorona, ya Allah Ka kiyayeni ta gabana, da bayana, da damana, da haguna, da samana, ina nemn tsarinKa kada a yaudareni da kisa ta ƙarƙashina".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance ba yana barin waɗannan addu'o'in ba lokacin da Ya yi yammaci da lokacin da ya wayi gari: (Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya), da kuɓuta daga masassara da masifu da tsanance-tsanance na duniya, da sha'awowi da fitintinu cikin Addini (a duniya da lahira) magaggauciya da majinkirciya. (Ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwame) da shafe zunubai da ƙetare su. (da lafiya) da kuɓuta daga aibuka, (a Addini na) daga shirka da bidi'o'i da saɓo, (da duniya ta) daga masifu da cuta da sharruka, (da iyalaina) matana da 'ya'ya na da 'yan uwana, (da dukiya ta) dukiyoyi na da aiki na. (Ya Allah Ka suturta al'aurori na) da abinda ke cikina na aibuka da ɓaci da taƙaitawa Ka shafe zunubai na, (Ka amintar da tsorace -tsorace na) razani na da tsoro na. (Ya Allah Ka kiyaye ni) Ka tunkuɗe bala'i daga gare ni daga abubuwa masu cutarwa da masifu, (ta gaba na da baya na, da dama na, da hagu na, da sama na) inda ya roƙi Allah Ya kiyaye shi ta kowane bangare: domin cewa masifu da aibuka kaɗai suna samun mutum ne kuma suna fuskantar sa daga ɗaya daga waɗannan ɓangarorin. (Ina neman tsarinKa kada a kashe shi ni) shi ne a kamani bagtatan, in mutu ba tare da na sani ba (ta ƙarƙa shi na) sh ne in halaka ta kisfewa.

فوائد الحديث

Kiyayewa akan waɗannan kalmomin dan koyi da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Mutum kamar yadda shi abin umarta ne da roƙon Allah lafiya a cikin Addini kamar haka shi abin umarta ne da roƙonta a duniya.

Al-Ɗaibi ya ce: Ya game ɓangarori shida ne; domin cewa aibuka daga garesu ne, kuma yakai matuƙa a ɓangaren ƙasa dan munin aibukan daga gareta ne.

Abin da yafi a karanta zikirai, a safiya: Daga ɓollowar alfijir zuwa ɓullowar rana a farkon yini, haka kuma daga bayan la'asar zuwa kafin faɗuwar rana, idan ya faɗesu bayan hakan yana nufin: Ya faɗesu a safiya bayan ɗagawar walaha ya isar masa, idan ya faɗesu bayan azahar ya isar masa, idan ya faɗesu bayan Magariba ya isar masa, to wannan lokaci ne na zikiri.

Dalili bai yi nuni ba akan kasancewar zikiri yana da lokaci ayyananne ba a cikin dare kamar karanta ƙarshen ayoyi biyu daga Suratul Baƙarah cewa ita tana kasancewa ne da daddare bayan faɗuwar rana.

التصنيفات

Addu’o’I da aka samu daga Annabi