إعدادات العرض
Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace
Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace".
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو हिन्दी 中文 Kurdî Português Nederlands অসমীয়া Tiếng Việt ગુજરાતી Kiswahili አማርኛ پښتو සිංහල ไทย Tagalog മലയാളം नेपाली Magyar ქართულიالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake da sama da mace (ɗaya), bai yi adalci tsakanin matansa gwargwadon iko ba na daidaitawa tsakaninsu a ciyarwa da wurin zama da abin sawa da wurin kwana, cewa uƙubarsa a ranar alƙiyama ta kasance ne rabin jikinsa a karkace, kuma karkacewarsa uƙuba ce gare shi akan zalincinsa, kamar yadda ya karkata a cikin mu'amalarsa.فوائد الحديث
Wajabcin raban kwana akan namiji tsakanin matansa biyu ko matansa da yawa, kuma karkata zuwa ga ɗayansu ya bar sauran yana haramta, a abinda yake da iko akansa na ciyarwa, da wurin zama, da kyakkyawar tarba, da makamancin hakan.
Daidaito a rabon kwana da makamancin haka, a abinda mutum yake iya mallakarsa, amma a abinda ba ya iya mallakinsa kamar soyayya da karkata ta zuciya to cewa shi ba ya shiga cikin hadisin, kuma shi ne abin nufi a cikin faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Ba zaku iya adalci a tsakanin mata ba koda kun yi kwaɗayi} [al-Nisa'i: 129].
Sakayya tana kasancewa ne daga jinsin aiki, cewa mutum a lokacin da ya karkata a duniya daga wata mace zuwa wata, zai zo a ranar alƙiyama ɗaya daga tsagin jikinsa ya karkace daga ɗayan.
Girmama haƙƙoƙin bayi, kuma cewa ba'a kau da kai a kansu; domin cewa su ababen ginawa ne akan ƙwauro da sakayya.
An so taƙaituwa akan mace ɗaya idan namiji ya ji tsoron kada ya yi adalci tsakanin matansa; dan kada ya faɗa a cikin gazawa a cikin Addini; Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba to (ku auri mace) ɗaya} [al-Nisa'i: 3].
التصنيفات
kyawawan Halayya tsakanin Ma'aurata