إعدادات العرض
Babu wani mutum da zai yi mini sallama har sai Allah Ya dawo mini da raina har sai na mayar masa da sallamar
Babu wani mutum da zai yi mini sallama har sai Allah Ya dawo mini da raina har sai na mayar masa da sallamar
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Babu wani mutum da zai yi mini sallama har sai Allah Ya dawo mini da raina har sai na mayar masa da sallamar".
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Español Kurdî Português සිංහල Nederlands অসমীয়া Tiếng Việt Kiswahili ગુજરાતી አማርኛ پښتو ไทย Română മലയാളം Deutschالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa shi ana dawo masa da ransa dan ya amsa sallama ga dukkan wanda ya yi masa sallama , daidai ne ya kasance a kusa yake ko a nesa; rayuwar barzahu da ƙabarbura wani al'amari ne na gaibu, babu wanda ya san haƙiƙaninsu sai Allah, Shi Mai iko ne akan dukkan komai.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa akan yawaita salati da sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Rayuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin ƙabarinsa ita ce mafi cikar rayuwar da mutum zai rayu a cikin barzahunsa, babu wanda ya san haƙiƙaninta sai Allah - Maɗaukakin sarki -.
Hadisin babu wata hujja a cikinsa ga wanda yake faɗin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rayuwa kamar yadda muke rayuwa, har ma'abota shirka suke kafa hujja da shi akan neman agaji da shi - tsira da amincin su tabbata agare shi -, kawai ita rayuwa ce ta barzahu.
التصنيفات
Abubuwan da Annabi ya kevanta da su