Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta:…

Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta: Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta: Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga ɗabi'u huɗu idan sun taru a tare da musulmi to ya zama mai tsananin kama da munafukai saboda waɗannan ɗabi'un, wannan ga wanda galibi suka zama a tare da shi akwai waɗannan ɗabi'un, amma wanda suka zama kaɗan to bai shiga cikin su ba, sune: Na farko: Idan zai yi zance sai ya yi gangancin ƙarya da rashin gaskiya a cikin zancensa. Na biyu: Idan aka yi yarjejeniya da shi ba zai cika ba, kuma ya yaudari abokinsa. Na uku: Idan ya yi alƙawari ba zai cika shi ba kuma sai ya saɓa shi. Na huɗu: Idan aka yi faɗa da shi kuma ya yi rigima tare da wani sai husumarsa ta zama mai tsanani, kuma ya bauɗe daga gaskiya, ya yi dabarar a kin karbar gaskiya da ɓata ta, kuma ya faɗi ɓata da ƙarya. Domin munafunci shi ne bayyanar da sabanin abinda aka ɓoye, wannan ma'anar samammiya ce a tare da mai waɗannan ɗabi'un, kuma munafuncinsa ya zama a cikin haƙƙin wanda ya zantar da shi, kuma ya yi masa alƙawari, ya amince masa, ya yi husuma da shi, ya yi yarjejeniya da shi cikin mutane, ba wai cewa shi munafuki ne a cikin musulunci ba sai ya bayyanar da shi alhali shi yana ɓoye kafirci, wanda ya kasance a cikinsa akwai wata ɗabi'a daga waɗannan ɗabi'un; to a cikinsa akwai siffa ta munafunci har sai ya barta.

فوائد الحديث

Bayanin sashin almomin munafuki dan tsoratarwa da gargaɗarwa daga afkawa a cikinsu.

Abin nufi daga Hadisin: Cewa waɗannan ɗabi'un sune ɗabi'un munafunci, kuma mai su mai kama da muanfukai ne a cikin waɗannan ɗabi'un, kuma mai ɗabi'antuwa ne da ɗabi'unsu, ba dan cewa shi munafuki ne mai bayyanar da musulunci ya ɓoye kafirci ba, an ce wannan abin ɗauka ne ga wanda waɗannan ɗabi'un suka rinjaye shi kuma ya yi sakaci da su, ya wulaƙantar da al'amarinsu; wanda ya zama kamar hakan to ya zama mai ɓatacciyar aƙida a galibi.

AlGazali ya ce: Asalin addini mai taƙaituwa ne a cikin abubuwa uku: Faɗa, da aikatawa, da niyya.

Sai ya faɗakar akan ɓacin magana da ƙarya, da kuma ɓacin aiki da ha'inci, da kuma ɓacin niyya da saɓawa alkawari; domin cewa saɓa alƙawari ba ya kawo cikas sai dai idan ƙudirin niyyar akansa ya kasance mai gwamuwa da alƙawari, amma da ya kasance mai ƙudirin niyya da gaske sai wani abu mai hanawa ya bijiro masa ko wani ra'ayi ya bayyana gare shi to wannan ba'a samu surar munafunci daga gare shi ba.

Munafunci nau'i biyu ne: Munafunci na aƙida yana fitar da mai shi daga imani, shi ne bayyanar da Musulunci da ɓoye kafirci. Da munafunci na aiki, shi ne kamanceceniya da munafukai a cikin ɗabi'unsu, wannan ba ya fitar da mai shi daga imani, sai dai cewa shi babban laifi ne daga manyan laifuka.

Ibnu Hajar ya ce: Haƙiƙa malamai sun haɗu akan cewa wanda ya zama mai gaskiya da zuciyarsa da harshansa kuma ya aikata waɗannan ɗabi'un ba'a yi masa hukunci da kafirci, kuma shi ba munafukin da za'a dawwamar a cikin wuta bane.

AlNawawi ya ce: Wasu jama'a daga malamai sun ce: Abin nufi munafukan da sun kasance a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka zantar da imaninsu, kuma suka yi ƙarya, kuma aka amince musu akan addininsu sai suka yi ha'inci, kuma suka yi alƙawari a cikin al'amarin addini suka taimake shi sai suka saɓa, kuma suka fajircewa abokanan husumarsu.

التصنيفات

Munafunci, Zargin Savo, Abubuwan da aka hana furtawa da kuma Illar Harshe