Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji

Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ni'ima da farin ciki da kyau a duniya, kuma Allah Ya isar da shi zuwa ni'imar aljanna da ni'imarta a lahira; ga wanda ya ji zancensa sai ya haddace shi har ya isar da shi ga waninsa, sauda yawa wanda aka isarwa hadisin ya zama ya fi kiyayewa kuma ya fi fahimta kuma ya fi ikon yin istinbaɗi daga wanda ya ruwaito hadisin, sai na farkon ya zama yana kyautata hadda da dakkowa, na biyun kuma ya zama yana kyautata fahimta da istinbaɗi (tsamo hukunci).

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan haddace sunnar Annabi, da isar da ita ga mutane.

Bayanin falalar ma'abota hadisi, da ɗaukakar nemansa.

Falalar malamai waɗanda sune ma'abota istinbaɗi da fahimta.

Falalar sahabbai - Allah Ya yarda da su -, su ne waɗanda suka ji hadisin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma suka isar da shi garemu.

AlManawi ya ce: Ya bayyana anan cewa maruwaicin hadisi Fiƙihu ba sharaɗinsa ba ne, sharaɗinsa kawai shi ne hadda, kuma ya wajaba ga masanin fiƙihu fahimta da jujjuya ma'ana.

Ibnu Uyaina ya ce: Babu wani da zai nemi hadisi sai a fuskarsa akwai ni'ima ga wannan hadisin.

Hadda a wajen malaman hadisi nau'i biyu ce: Hadda ta zuciya da ƙirji, da hadda ta rubutu da zanawa, su biyun addu'ar a cikin hadisin ta ƙunshe su.

Fahimace-fahimcen mutane mabanbanta ne, wataƙila wanda aka isarwa ya zama ya fi kiyayewa daga wanda ya ji, da yawa wanda ya dakko fiƙihu ya zama ba faƙihi ba.

التصنيفات

Falalar Ilimi, Ladaban Malami da Xalibi