إعدادات العرض
Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne
Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, mu muna tafiya a teku, kuma muna ɗaukar ruwa kaɗan tare da mu, idan muka yi alwala da shi zamu ji ƙishirwa, shin zamu yi alwala daga ruwan kogi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt Kurdî Português සිංහල Nederlands অসমীয়া Kiswahili ગુજરાતી አማርኛ پښتو ไทย Română മലയാളം Deutsch Oromoo नेपाली ქართულიالشرح
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Lallai mu muna hawa jiragen ruwa a cikin kogi dan sū ko kasuwanci da abinda ya yi kama da hakan, kuma muna ɗaukar ruwa kaɗan wanda za'a iya sha, idan muka yi anfani da ruwan shan dan yin alwala da wanka zai ƙare, kuma ba zamu samu wanda zamu sha ba, shin ya halatta garemu mu yi alwala da ruwan kogi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce game da ruwan kogi: Ruwansa mai tsarki ne kuma mai tsarkakewa; alwala tana halatta da shi da kuma wanka da shi, kuma halal ne cin abinda yake fita daga cikinsa na kifaye da wasunsu, koda an samu mushe ya fito a bayansa ba tare da an yi sū dinsa ba.فوائد الحديث
Mushen dabbar kogi halal ne, abin nufi da mushensa: Abin da ya mutu a cikinsa na dabbobinsa daga abinda ba ya rayuwa sai a cikinsa.
Amsawa mai tambaya da mafi yawan abinda ya tambaya dan cika fa'ida.
Abin nufi idan ɗanɗanonsa ko launinsa ko warinsa ya canja da wani abu mai tsarki, to shi wanzajje ne akan tsarkinsa muddin dai ruwa ne wanzajje akan haƙiƙaninsa, ko da tsartsinsa ko zafinsa ko sanyinsa ko waninsa ya tsananta.
Ruwan kogi yana ɗauke babban kari da karami, kuma yana gusar da najasa wacce da ta afkawa abu mai tsarki, daga jiki, ko tufa, ko wanin hakan.
التصنيفات
Hukunce Hukuncen Ruwa