Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta

Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta

Daga Abu sa'id AlKhudr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance ya yi yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yaƙi goma sha biyu - ya ce: Na ji abubuwa hudu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka ƙayatar dani, ya ce: "Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta, Babu azumi a ranaku biyu: Karamar sallah da babbar sallah, kuma babu sallah bayan asuba har sai rana ta bullo, kuma babu bayan la'asar har sai ta fadi, kuma ba'a daure sirdi (nikar gari domin tafiya) sai a masallatai uku: Masallaci mai alfarma, da masallacin Kudus, da masallacina wannan".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana abubuwa hudu: Na farkonsu: Hana mace daga tafiyar kwana biyu ba tare da mijinta ba ko daya daga muharramanta ba, shi ne wanda ta haramta agare shi haramci na har'bada daga 'yan uwa, kamar Da, da uba, da Dan dan uwa da dan 'yar uwa, da baffa da kawu, da makamancin hakan. Na biyunsu: Hani daga azimin ranar ƙaramar sallah da ranar babbar sallah, duk daya ne musulmi ya azimce su ne akan bakance (alwashi) ko nafila, ko kuma kaffara. Na ukunsu: Hani daga sallar nafila bayan sallar la'asar har sai rana ta fadi, da bayan bullowar alfijir har sai rana ta bullo. Na hudunsu: Hani daga tafiya zuwa wani wuri daga wurare da ƙudirce falalarsu da ƙudirce ninkin kyawawan lada a cikinsu, in banda wadannan masallatan uku, to ba'a daure sirdi ga wasunsu dan yin sallah a cikinsu, domin lada ba'a ninkashi sai a wadannan masallatan uku: Masallaci mai alfarma (Dake Makka), da masallacin Annabi (Dake Madina), da masallacin Kudus (Dake Falasdin).

فوائد الحديث

Rashin halaccin tafiyar mace ba tare da muharrami ba.

Mace ba muharrama ba ce ga mace a tafiya; Saboda fadinsa: "Mijinta ko muharraminta".

Dukkan abinda ake kira tafiya to mace an hanata ta yi ba tare da miji ko muharrami ba, wannan hadisin ya kasance ne gwargwadan halin mai tambaya da wurinsa.

Muharamin mace shi ne mijinta ko wanda ya haramta ta aure shi har abada, saboda kusanci kamar uba da Da da baffa da kawu.

Ko shayarwa kamar uba na shayarwa da baffa na shayarwa, ko surukuta kamar baban miji, kuma ya zama musulmi baligi mai hankali amintacce, domin abin nufi daga muaharrami kare mace da tsareta da tsayuwa da sha'aninta.

Kulawar shari'ar Musulunci da mace, da kareta da tsareta.

Rashin ingancin sallar nafila kowacce bayan sallar Asuba da la'asar, an toge daga hakan rama farillan da suka wuce, da masu sabubba, kamar gaisuwar masallaci da makamancin hakan.

Sallah ta haramta bayan bullowar rana kai tsaye, domin babu makawa sai ta dago gwargwadan goron mashi, da abinda ya yi kusa na mintina goma zuwa sha biyar a kusance.

Lokacin la'asar yana mikewa zuwa faduwar rana.

A cikinsa akwai halaccin daure sirdi (domin tafiya) zuwa masallatai uku.

Falalar masallatai uku da fifikonsu akan wasunsu.

Rashin halaccin tafiya dan ziyartar ƙaburbura koda ya kasance ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ne, amma ziyararsa ta halatta ga wanda yake a Madina, ko ya zo Madina dan wata buƙatar da aka shara'anta ko aka halatta.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Masallacin Harami da Masallacin Manzon Allah da Baitilmaqdas, Hukunce Hukuncen Mata, Tarihin Makkah da Madina da Al-Aqsa