Kada ku zagi Sahabbaina, da ace xayanku zai ciyar da Zinare kwatankwacin Dutsen Uhudu ba zai kai cikin Mudunsu ko kuma rabinsa

Kada ku zagi Sahabbaina, da ace xayanku zai ciyar da Zinare kwatankwacin Dutsen Uhudu ba zai kai cikin Mudunsu ko kuma rabinsa

Daga Abu Sai'd -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Kada ku zagi Sahabbaina, da ace xayanku zai ciyar da Zinare kwatankwacin Dutsen Uhudu ba zai kai cikin Mudunsu ko kuma rabinsa"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Manzon Allah ya hana a Zagi sahabbansa kuma ya bada labarin cewa da ace wani daga cikin Mutane zai ciyar da girman Dutsen Uhudu na zinare to ba zai kai cikin tafin hannunsu ko tabimsa ma, saboda Sahabbai sune Mafi girman Daraja daga waxanda suka zo bayansu,kuma Dalilin fifita ciyarwasu shi ne ta kasance lokacin lalura be da kuma rashin abun hannu saboda kuma ciyarwarsu don taimakon manzon Allah SAW ne da kuma kare shi, kuma babu shi abayan rayuwasa, haka na Jihadinsu da sauran Ayyukansu, tare da abunda yake cikin zukatansu na tausayi da kauna da tsoron Allah da qanqan da kai da kuma fifita waninsu akansu, da Jahadi a tafarkin Allah iya yinsu, ga falalar Zama da Manzon Allah koda kuma Xan lokaci ne to babu wani aiki da zaikai hakan kuma da falaloli waxanda ba za'a iya qiyasta su ba wancan Falalar Allah ce yana bada ita ga wanda ya so

التصنيفات

Qudurcewa ga me da Sahabbai -Amincin Allah a gare su-