cewa an sami wata mata a kashe a cikin wani sashi daga cikin yakokin annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi

cewa an sami wata mata a kashe a cikin wani sashi daga cikin yakokin annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi

Daga Abdullahi dan umar- Allah ya kara yarda a garesu su biyun- { Cewa tabbas an sami wata mata da aka kashe a cikin wani sashi daga cikin yakokin annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi, sai annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi yayi inkarin kashe mata, da yara }.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Hanin annabi mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da yayi na kashe mata da yara yana nuninbisa haramcin kashe su, fadar sa a cikin wani sashin hadisan da suka zo cikin wannan ma`ana: (Bai dace wannan dai tayi yaki ba) fadakarwa ce bisa illar hani dangane da hana kashe mata; saboda mafi rinjaye a cikin su basa yin yaki duk da kasancewar wasu a cikin su suna da sharri da jarumta saidai hukuncin an rataya shi bisa mafi rinjayensu, amma duk wadda tayi yaki a cikin su sai a yake ta.

التصنيفات

Ladaban Jihadi