Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu…

Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: "Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"

[Ingantacce ne]

الشرح

Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: (Ya Allah gareKa ne na miƙa wuya) kuma na jawu, (da Kai ne na yi imani) na gasgata kuma na yi iƙrari, (kuma gareKa ne na dogara) na fawwala na kuma dogara, (gareKa ne na koma) na koma na fuskanta, (saboda Kai ne na yi husuma) na yi jayayya da maƙiyanKa, (Ya Allah ni ina neman tsarinKa) ina fakewa (da buwayarKa) da hanawarKa da kuma rinjayenKa, (babu abin bautawa da gaskiya sai Kai) kuma babu wani abin bautawa da gaskiya inba Kai ba, (da Ka ɓatar da ni) daga shiriya da dacewa da yardarKa, (Kai ne Rayayye wanda ba zai mutu ba) kuma ba zai ƙareba, (aljanu da mutane kuwa zasu mutu).

فوائد الحديث

Halaccin gabatar da yabo (ga Allah) a yayin roƙon kowane abin nema.

Wajabcin dogara ga Allah - Maɗaukakin sarki - Shi kaɗai da neman kiyayewa daga gareShi; domin cewa Shi Mai siffantuwa ne da siffofin cika, kuma Shi kaɗaine wanda ake dogara da Shi, halittu dukkaninsu gajiyayyu ne kuma masu tiƙewa ne zuwa ga mutuwa, su basu cancanci dogara a kansu ba.

Koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin addu'a da waɗannan kalmomi masu tattarowa komai ya shiga, waɗanda suke bayyanar da gaskiyar imani da kuma matuƙar sakankancewa.

Sindi ya ce: Faɗinsa (Kai ne Rayayye) wato: Kai ne wanda ya kamata a nemi tsari da Shi ba waninKa ba.

التصنيفات

Koyarwar Manzon Allah SAW a cikin Zikiri, Addu’o’I da aka samu daga Annabi