Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta

Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi kabbarar sallah yana yin shiru kaɗan kafin ya karanta fatiha, yana buɗe sallarsa da wasu daga addu'o'i a cikinta, daga abinda ya zo daga waɗannan addu'o'in faɗinsa: "Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti, ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwa da ƙanƙara da ruwa mai tsananin sanyi". Shi yana roƙon Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya nisantar da tsakaninsa da kurakurai da kada ya faɗa cikinsu, nisantarwa ta inda gamuwa ba zata ƙara faruwa tare da shi ba, kamar yadda babu haɗuwa tsakanin mahudar rana da mafaɗarta har abada, idan kuma ya faɗa cikinsu to Ya tsaftace su Ya kawar da su kamar yadda ake kawar da datti daga farin tufa, kuma Ya wanke shi daga kurakuransa Ya sanyaya horuwarsu da zafinsu, da waɗannan masu tsaftacewar masu sanyi: Ruwa, da kankara, da sanyi.

فوائد الحديث

Boye addu'ar buɗe sallah koda sallar ta kasance ta karatun bayyana ne.

Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan sanin halayen Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a motsinsa da shirunsa.

Wasu sigogin daban sun zo na addu'ar buɗe sallah, abinda ya fi shi ne mutum ya bibiyi addu'o'in buɗe sallah da suka zo, kuma tabbatattu daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma ya zo da wannan.

التصنيفات

Zikirin Sallah