إعدادات العرض
Idan ɗayanku ya isa zuwa ga majalisa to ya yi sallama, idan kuma yana so ya tashi to ya yi sallama, domin (sallama) ta farkon bata fi mafi cancanta daga ta ƙarshe ba
Idan ɗayanku ya isa zuwa ga majalisa to ya yi sallama, idan kuma yana so ya tashi to ya yi sallama, domin (sallama) ta farkon bata fi mafi cancanta daga ta ƙarshe ba
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya isa zuwa ga majalisa to ya yi sallama, idan kuma yana so ya tashi to ya yi sallama, domin (sallama) ta farkon bata fi mafi cancanta daga ta ƙarshe ba".
[Hasan ne] [Al-Nasa'i Ya Rawaito shi]
الشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da wanda ya zo wurin zaman mutane da ya yi musu sallama, idan kuma ya yi nufin ya tashi daga wurin to ya yi wa mutanen wurin bankwana da yin sallama; dan sallamar farkon lokacin zuwa ba ta fi mafi cancanta daga ɗayar sallamar a lokacin da zai bar wurinba.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa akan yaɗa sallama.
Kwaɗaitarwa akan yin sallama ga mutanen dake zaune a lokacin haɗuwa da kuma lokacin juyawa.
Sindi ya ce: Faɗinsa: (Idan ya yi nufin tashi) wato: Daga majalisar. (To ta farkon bata kasance mafi cancanta ba) wato: Su biyun gaba ɗayansu sunnah ne da yin aiki da su, dan haka babu wata fuska ga barin ta biyu tare da tabbatar data farkon.
التصنيفات
Ladaban Sallama da Neman izini