Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka, sannan ya tsettsefe gashinsa da hannunsa har sai ya tabbar cewa ya jika fatarsa, sai ya zuba ruwa akansa sau uku, sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Ta ce: Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya daya muna kanfatowa daga gareta gaba daya.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin wankan janaba sai ya fara wanke hannayensa, sannna ya yi alwala kamar yadda yake alwalar sallah, sannan ya zuba ruwa a jikinsa, sannan ya tsattsefe gashin kansa da hannayensa, har sai ya tabbar cewa ruwa yakai tushen gashin, ya jika fatar, sai ya zuba ruwa akansa sau uku sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kwarya daya, muna kanfatowa daga gareta gaba daya.

فوائد الحديث

Wanka (Wankan tsarki) nau'i biyu ne: Mai isarwa da kuma cikakke, amma mai isarwa sai mutum ya yi niyyar tsarki, sannan ya game jikinsa da ruwa tare da kuskurar baki da shaka ruwa.

Amma cikakken wanka sai ya yi wanka kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wanka a wannan hadisin.

Ana anfani da lafazin janaba ga dukkanin wanda ya fitar da maniyyi, ko ya tara da matarsa koda bai yi maniyyi ba.

Halaccin kallon daya daga ma'aurata al'aurar dayan, da kuma wankansu daga kwarya daya.

التصنيفات

Wanka, Wanka