Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa

Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa

Daga Nu'uman dan Bashir - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasansa sun kasance idan sun nemi ashayar da su ruwa sai sun wuce wadanda ke samansu, sai suka ce: Dama a ce zamu tsaga wata kafa a rabonmu ba mu cutar da wandanda ke samanmu ba, idan sun barsu da abinda suka yi nufi za su halaka gaba dayansu, idan suka yi riko da hannayensu za su tsira, sai su tsira gaba dayansu".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya buga misali ga tsayayyu akan dokokin Allah, masu tsayawa akan umarnin Allah, masu horo da aikin alheri, masu hani daga abin ki, da misalin masu afkawa dokokin Allah masu barin kyakkyawan aiki, masu aikata abin ki, da tasirin hakan a nasarar zamantakewar jama'a, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka hau jirgin ruwa, sai suka yi kuri'a ga wanda zai zauna a saman jirgin ruwan da wanda zai zauna a kasansa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasa idan sun so samun ruwa sai sun wuce ta wurin wadanda ke saman, sai wadanda ke kasa suka ce: Da a ce zamu tsaga wata tsaga a daidai wurin mu a kasa mu dinga samun ruwa daga gareshi, har ya zama bamu cutar da wanda ke samanmu ba, da a ce wadanda ke sama sun barsu su aikata hakan da jirgin ruwan ya nitse da su gaba daya, da a ce sun hanasu hakan da duk jama' biyun sun tsira.

فوائد الحديث

Muhimmancin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki a kiyaye zamantakewar jama'a da kuma tsiransu.

Daga hanyoyin koyarwa akwai buga misalai, dan kusanto da ma'anoni ga hankula kamar ga abin.

Aikata abin ki a zahiri tare da kin yin inkari akansa barna ce da zata cutar da kowa da kowa.

Halakar jama'a tana kasance wa ne akan barin ma'abota barna suna barna a bayan kasa.

Aiki na kuskure da kyakkyawan niyya ba sa isuwa a gyaruwar aiki.

Nauyin aiki a cikin jama'ar musulmi na gaba daya ne, ba'a rataya shi ga wani ayyananan mutum.

Azabtar da kowa da kowa saboda zunuban wasu mutane idan ba a yi hanani ba.

Masu aikata mummunan aiki suna bayyanar da mummunan aikinsu mai makon su yi alheri ga jama'a kamar munafukai.

التصنيفات

Falalar Umarni da kyakkyawan aiki da hani da Mummuna