إعدادات العرض
Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa
Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa
Daga Ammar dan Yasir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikeni wata bukata, sai na samu janaba ban samu ruwa ba, sai na tumurmusa a bigire kamar yadda dabba take tumurmusa , sannan na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na ambata masa hakan sai ya ce: "Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa.
[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt ئۇيغۇرچە Português Kurdî Kiswahili සිංහල Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá پښتو অসমীয়া دری Кыргызча or Malagasy नेपाली Čeština Oromoo Română Nederlands Soomaali తెలుగు മലയാളം Lietuvių Српски ไทย Kinyarwanda Shqip ಕನ್ನಡ Wolof Українська Moore ქართული Magyarالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki Ammar Dan Yasir - Allah Ya yarda da shi - a wata tafiya dan wasu bukatunsa, sai janaba ta same shi ta hanyar jima'i ko zubar maniyyi da sha'awa, bai samu ruwa ba da zai yi wankan (janaba) ba., ya kasance bai san hukuncin taimama dan janaba ba, kadai yana da sanin hukuncinta ne dan karamin kari ne, sai ya yi ijtihadi ya yi zatan cewa kamar yadda zai shafi sashin gabban alwala daga karamin kari da turbayar dake doron kasa, to babu makawa taimama daga janaba ta kasance da game jiki da turbaya; dan kiyasi akan ruwa, sai ya jujjuya a cikin turbaya har ya game jiki ya yi sallah, lokacin da ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ambata masa hakan; dan ya ga shin akan daidai yake ko a'a? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana masa siffar tsarkaka daga karamin kari kamar fitsari, da babban kari kamar janaba: Shi ne ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa.فوائد الحديث
Wajabcin neman ruwa kafin taimama.
Halaccin taimama ga wanda ke da janaba bai samu ruwa ba.
Taimama dan babban kari, kamar taimama ne dan karamin kari.
التصنيفات
Taimama