Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku

Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku

Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku kuma mafi alheri agareku daga ciyar da zinari da azirfa, kuma mafi alheri agareku daga ku haɗu da maƙiyanku ku daki wuyan su, suma su daki wuyan ku?" suka ce: Eh. Ya ce: "Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: . Shin kuna son in baku labari ? In sanar da ku da mafificin ayyukanku, kuma mafi ɗaukakarsu, mafi ƙaruwarsu, mafi tsarkinsu, mafi tsaf-tsaf ɗinsu a wurin Allah Mamallaki - Mai girma da ɗaukaka -? . kuma mafi ɗaukakarsu a cikin masaukanku a aljanna? kuma mafi alheri gareku daga sadaka da zinare da azirfa? Kuma mafi alheri a gareku daga ku haɗu da kafirai dan yaƙi, sai ku daki wuyansu, su daki wuyanku ? Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkan lokuta da kuma dukkan siffofi da halaye.

فوائد الحديث

Cewa dawwama akan ambaton Allah - Maɗaukakin sarki - a zahiri da baɗini yana daga mafi girman kusanci, kuma mafi anfaninsu a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Dukkan ayyuka kawai an shara'antasu ne dan tsaida ambaton Allah - Maɗaukkain sarki -, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ka tsaida sallah dan ambatona}. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kaɗai an sanya Dawafi a ɗaki da kuma tsakanin Safa da Marwa, da jifan Jammarat (Shaiɗanu) dan ambatan Allah ne - Maɗaukakin sarki -. Abu Dawud ne da Tirmizi suka fitar da shi.

Izzu ɗan Abdussalam ya faɗa a cikin Kawa'idinsa; Wannan Hadisin yana daga abinda yake nunarwa cewa lada ba ya jerantuwa akan gwargwadan wahala a dukkanin ibadu. Kawai Allah - Maɗaukkain sarki - Zai iya bada lada mai yawa akan aiki ɗan kaɗan sama da yadda zai bada lada akan aiki mai yawa.

Lada yana jerantuwa akan banbancin darajoji a matsayi.

AlManawi ya faɗa a cikin Faidil Kadir: Wannan Hadisin za’a ɗauke shi ne akan zikiri ya kasance mafifici ga waɗanda ake magana da su. Da za’a yi magana da wani gwarzo sadauki wanda amfanin musulunci zai samu da shi a cikin yaƙi da an ce da shi yaƙi, ko mawadacin da talakawa za su anfana da dukiyarsa da an ce da shi sadaka, mai iko akan Hajji da an ce da shi Hajji, ko wanda yake da iyaye da an ce da shi yi musu biyayya, da wannan ne za’a haɗa tsakanin Hadisan.

Mafi cikar zikiri abinda harshe ya furta shi tare da Tadabburin zuciya (ma'anoninsa), sannan abinda yake kasancewa da zuciya ita kaɗai kamar tunani, sannan abinda ya kasance da harshe shi kaɗai, a kowanne akwai lada in Allah Ya so - Maɗaukakin sarki -.

Lazimtar musulmi zikiran da suke da lokuta da kuma yanayi kamar zikiran safiya da maraice, da shiga masallaci da gida, da bayan gida da fita daga cikinsu... da wanin hakan zai sanya shi daga masu ambatan Allah da yawa.

التصنيفات

Falalar Zikiri