Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a buɗe muku na ƙawar duniya da adonta

Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a buɗe muku na ƙawar duniya da adonta

Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zauna wata rana akan minbari muma muka zauna a gefensa, sai ya ce: "Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a buɗe muku na ƙawar duniya da adonta" sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, shin alheri yana zuwa da sharri ne? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shiru, sai akace masa: Meke damunka ne? kana yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma bai kulaka ba ? sai mukaga cewa can ana saukar me (da wahayi) ne? ya ce: Sai ya shafe gumi daga gare shi , sai ya ce: "Ina mai tambaya?" kamar shi ya yabe shi , sai ya ce: "Lallai alheri ba ya zuwa da sharri, yana daga abinda kaka take tsirarwa (akwai) abinda yake kashewa ko ya aibata, sai masu cin ciyayi, sun ci har saida kwiɓinansu suka cika sai suka fuskanci idan rana, sai suka yi toroso suka yi fitsari, suka yi kiwo, lallai wannan dukiyar koriyace mai zaƙi, madalla da na musulmi abinda aka bawa miskini daga gareta da maraya da ɗan matafiyi - ko kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata ya ce -: Kuma cewa shi wanda ya ɗauketa ba tare da haƙƙinta ba, to kwatankwacinsa kamar wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, zata zama mai yi masa shaida ranar alƙiyama".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wata rana Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zauna akan minbari yana karantar da sahabbansa sai ya ce: Lallai cewa mafi yawancin abinda nake jiye muku tsoro a bayana (shi ne) abinda za'a buɗa muku na albarkatun ƙasa da ƙawace-ƙawacen duniya da adonta da kyanta, da abinda ke cikinta na nau'ikan jin daɗi da tufa da shukoki da wasunsu daga abinda mutane suke alfahari da kyawunsu tare da ƙarancin wanzuwa. Sai wani mutum ya ce: Kawace-ƙawacen duniya ni'imace daga Allah, shin wannan ni'imar zata dawo ta zama azaba da uƙuba?! Sai mutane suka zargi mai tambayar yayin da suka gan shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shiru, suka zaci cewa ya fusatar da shi ne. Sai ya bayyana cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance wahayi yana saukar masa ne, sannan ya fara shafe gumi daga goshinsa, sai ya ce: Ina mai tambaya? Ya ce: Ni ne. Sai ya godewa Allah ya yi yabo a gareShi, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Alheri na haƙiƙa ba ya zuwa da (komai) sai da alheri, sai dai waɗannan ƙawace-ƙawacen ba tsantsar alheri bane saboda abinda suke kaiwa gare shi na fitina da gasa da shagaltuwa da su daga cikar fuskantar lahira, sai ya buga misali ga hakan sai ya ce: Lallai tsiron kaka da korensa, shi wani nau'i ne na shuka da yake ƙayatar da dabbobi sai ya yi kisa dan yawan ci da cikaciki ko ya kusa yin kisa, sai (dabba) mai cin koriyar ciyawa ta ci har ta cika kwiɓinan cikinta, sai ta fuskanci rana ta yi toroso daga cikinta a sirance ko ta yi fitsari, sannan ta nemi daga abinda ke cikin hantarta sai ta tauna shi sannan ta hadiye shi, sannan ta dawo sai ta cinye. Domin cewa wannan dukiyar kamar maɓungura ƙasane koraye mai zaƙi, yana kisa ko yana kusa ya yi kisa saboda yawansa; sai dai idan ya taƙaita daga gare shi akan kaɗan ɗin da buƙatuwa take isa zuwa gareshi, kuma isuwa take samuwa da shi ta hanyar halal domin cewa shi ba ya cutarwa, madalla dana musulmi wanda shi ga wanda ya ba wa miskini da maraya da matafiyi daga gareta, wanda ya karɓeta da haƙƙinta za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta ba tare da haƙƙinta ba to kwatankwacinsa kamar kwatankwacin wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, kuma zata zama mai shaida akansa a ranar alƙiyama.

فوائد الحديث

Al-Nawawi ya ce: A cikinsa: (Akwai) falalar dukiya ga wanda ya riƙeta da haƙƙinta da kuma kasheta ta fuskokin alheri.

Bayanai daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da halin al'ummarsa, da kuma abinda za'a buɗe musu na ƙawace-ƙawacen rayuwar duniya da fitintinunta.

Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - buga misali dan kusanto da ma'anoni.

Kwaɗaitarwa akan sadaka da sarrafa dukiya a bangarorin alheri, da kuma tsoratarwa daga kamewa (rowa).

Za'a ɗauka daga faɗinsa: "Lallai cewa shi alheri ba ya zuwa da sharri" lallai cewa arziƙi koda ya yi yawa to shi yana daga jumlar alheri, kaɗai sharri yana bijirowane da mai bijirowar rowa da shi ga wanda yake cancantarsa, da ɓarnatarwa a ciyar da ita a abinda ba'a shara'anta ba, kuma kowane abu (wanda) Allah Ya hukunta ya zama alheri to ba ya zama sharri da akasin haka, sai dai ana jin tsoro ga wanda aka azirta masa alheri abinda zai iya jawo sharri ya bijiro masa a cikin tasarrufinsa.

Barin gaggawa a wurin bada amsa idan ta kasance yana buƙatuwa zuwa lura.

Al-Ɗaibi ya ce: Ana ɗaukar nau'ika huɗu daga gare shi : Wanda ya ci daga gareta ci na jin daɗi mai yawaitawa mai zari har sai da haƙarƙarinsa ya buɗe ba ya tashi sai halaka ta yi gaggawa zuwa gare shi, wanda kuma ya ci kamar haka sai dai shi ya fara dabara dan kau da cuta bayan ya nemi hukuntawa sai ta rinjaye shi sai ta halaka shi, wanda ya ci kamar haka sai dai cewa shi ya yi gaggawa zuwa gusar da abinda zai cutar da shi kuma yana dabara a kau da shi har ya haɗiye sai ya kuɓuta, wanda ya ci alhali bai yawaita ba kuma bai yi zari ba, kawai ya taƙaita akan abinda zai toshe yunwarsa ya kame uwar hanjinsa, to na farkon misalin kafiri ne, na biyun kuma misalin mai sabo ne rafkananne daga cirata da tuba sai alokacin kuccewarta, na uku kuma misalin mai cakudawa ne mai gaggawa ga tuba yayin da zata zama abar karba, na hudun kuma mai gujewa duniya ne mai kwadayin lahira.

Ibnul Munir ya ce: A cikin wannan hadisin akwai fuskokin kamanceceniya masu ƙayatarwa, na farkonsu: Kamanta dukiya da ƙaruwarta da tsirrai da kuma bayyanarta.

Na biyunsu: Kamanta mai kutsawa a neman kuɗi da sabubba da dabbobi mai zari a cikin ciyawa.

Na ukunsu: Kamanta mai yawaitawa daga gareta da tanadinta da mai zari a cikin ci da cika ciki daga gareta.

Na huɗunsu: Kamanta mai fitowa daga dukiya tare da girmanta a cikin rayuka har ya kai zuwa kai ƙololuwa a rowa da ita da abinda dabbobi suke zubarwa na toroso, a cikinsa akwai nuni mai ƙayatarwa zuwa ƙazantar da shi a shari'a, na biyarɗinsu: kamanta wanda ya gaza tarata da tarota da akuya idan ta yi hutu sasanninta suka saraya, tana mai fuskantar idan rana; to cewa ita tana daga mafi kyan halayenta a nutsuwa da shiru, kuma a cikinsa akwai nuni zuwa riskarta dan maslahohinta.

Na shidansu: Kamanta dukiya da abokin da ba'a amintuwa ya juya zuwa maƙiyi; domin cewa dukiya daga sha'aninta a tsareta a ɗaure igiyarta dan sonta; hakan yana hukunta hanata daga wadanda suka cancanceta sai ta zama sababi ga uƙubar wanda yake tarata.

Na takwasɗinsu: Kamanta mai ɗaukarta ba tare da haƙƙi ba da wanda yake ci amma ba ya ƙoshi.

Sindi ya ce: Babu makawa a cikin alheri daga al'amura biyu, na farkonsu: Tabbatar da shi ta fuskarsa, na biyu: Juyar da shi a wuraren da ake juyar da shi, a yayin da ɗayan ya koru zai zama cuta...akan ce: A cikinsa akwai nuni zuwa lazimta tsakanin ƙaidi biyu; ba'a datar da mutum ga bayarwa a wuraren bayarwa sai idan ya karɓe shi ta inda ya dace.

التصنيفات

Zargin Son Duniya