إعدادات العرض
Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in
Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Português Kurdî සිංහල Tiếng Việt Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતી Nederlands አማርኛ ไทย മലയാളം Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya azumci wani yini a yaƙi, an ce a yaƙi da waninsa yana mai ikhlasi ga Allah dan neman sakamako da lada daga Allah; to lallai Allah da falalarsa Zai nisantar da tsakaninsa da tsakanin wuta (tsawon) shekara saba'in.فوائد الحديث
AlNawawi ya ce: Falalar azimi a tafarkin Allah, shi abin ɗauka ne akan wanda ba ya cutuwa da yin azumin, kuma ba zai salwantar da wani haƙƙi idan ya yi azumin, kuma yaƙinsa ko waninsa ba zai bata muhimman yaƙi da shi ba.
Zaburarwa da kwaɗaitarwa akan azimin nafila.
Wajabcin ikhlasi da neman yardar Allah, kuma kada ya yi azimi dan riya ko jiyarwa ko dan wasu manufofin daban.
Sindi ya ce: Faɗinsa (A tafarkin Allah), za'a iya ɗaukar cewa abin nufi mujarradin gyara niyya, kuma za'a iya ɗaukar cewa abin nufi da shi cewa shi ya yi azimi a halin kasancewarsa mai yaƙi, na biyun shi ne abin gaggawar (manufa).
Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa:
(Kharif saba'in) Kharif wani lokaci ne sananne a shekara, abin nufi da shi a nan shekarar (gaba ɗayanta), kuma keɓance Kharif (Kaka) da ambato banda ragowar lokutan - zafi da sanyi da damina -; domin cewa Kharif (Kaka) ya fi ragowar lokutan kyau domin kasancewarsa ana tsinkar 'ya'yan itatuwa a cikinsa.
التصنيفات
Azumin Taxawwu'i