إعدادات العرض
1- Kuma duk wanda yai Azumin kwana daya sabida Allah zai nisanta Fuskarsa daga Wuta daga Wuta tafiyar Damina Arba'in
2- Masoyina - Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayi mun wasiyya da abubuwa guda uku : Azumi uku a kowane wata, da raka'o'i biyu lokacin walaha, kuma da yin wuturi kafin inyi bacci
3- "Kayi Azumin Kwana Uku a kowane wata Kamar kayi Azumin zamani ne baki daya"
4- Cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- yayi Azumi Ranar Ashura
5- Lallai cewa Mafi Soyuwar Azumi A wajen Allah shi ne Azumin Annabi Dauda, kuma Mafi soyiwar Sallah Ita ce Sallar Annabi Dauda, ya kasance yana bacci rabin Dare, kuma ya tashi Daya bisa ukun Dare, kuma ya kara Bacci a Daya bisa Shidan Dare, kuma ya kasance yana Azumi yau kuma gobe ya Huta
6- Babu wani azumi sama da azumin dan uwana Dawud - wani bangare na zamani - yayi azumi wata rana bai azumci yini ba
7- "Manzon Allah -tsira da amincin Allah- ya kasance yana kirdadon Azumin Litinin da Alhamis"
8- Idan kayi Azumi Uku a kowane Wata kayi Azumin Sha Uku da Sha Huxu da Sha biyar