Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci

Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa masoyinsa kuma abokinsa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa wasicci kuma ya alkawaranta masa ɗabi'u uku: Na farko: Azimin kwana uku a kowane wata. Na biyu: Raka'a biyu ta walaha a kowace rana. Na uku: Witiri kafin bacci; hakan ga wanda ya ji tsoron kada ya farka a ƙarshen dare.

فوائد الحديث

Banbance - banbancen wasiyyoyin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa: Abin ginawa ne akan saninsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da halayen sahabbansa, da abinda yake dacewa da kowa daga cikinsu, mai ƙarfi yaƙi ya dace da shi, mai ibada bauta ta dace da shi, malami kuma ilimi ya dace da shi, haka dai.

Ibnu Hajar al-Askalani ya faɗa acikin faɗinsa: Azimin kwana uku daga kowane wata, abinda yake bayyana cewa abin nufi da su kwanukan fari; sune: Ranar goma sha uku, da goma sha huɗu, da goma sha biyar, daga watan Hijira.

Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: A cikinsa akwai son gabatar da witiri kafin bacci, hakan a cikin hakkin wanda bai aminta da farkawa ba.

Muhimmancin waɗannan ayyukan guda uku; saboda wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wani adadi daga sahabbansa.

Ibnu Daƙiƙul id ya faɗa a cikin faɗinsa: (Da raka'o'i biyu na walaha): Wataƙila cewa shi ya ambaci mafi ƙaranci ne wanda ake samun ƙarfafawa a aikata shi, a cikin wannan akwai nuni akan son sallar walaha, kuma cewa mafi ƙarancinta raka'a biyu ce.

Lokacin sallar walaha: Tun daga ɓullowar rana da kimanin ɗaya bisa huɗu na awa (kwata), kuma lokacinta yana miƙewa har zuwa kusan kafin lokacin azahar da minti goma, adadinta: Mafi ƙarancinta raka'a biyu ce, an yi saɓani a mafi yawanta; An ce: Raka'a takwas ce, ance: Babu iyaka ga mafi yawanta.

Lokacin witiri: Tun daga bayan sallar isshai'i har zuwa ɓullowar alfijir, kuma mafi ƙarancinsa raka'a ɗaya ne, mafi yawancinsa raka'a goma sha ɗaya ne.

التصنيفات

Azumin Taxawwu'i