إعدادات العرض
Wanda ya azimci zamani (a here) to bai yi azimi ba, azimin kwana uku azimin zamani ne gaba ɗayansa
Wanda ya azimci zamani (a here) to bai yi azimi ba, azimin kwana uku azimin zamani ne gaba ɗayansa
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai kai kana azimi tsawon shekara, kuma kana tsayuwar dare?", sai na ce: Eh, ya ce: "Lallai kai idan ka aikata hakan ido zai yi rauni saboda shi, kuma zuciya zata gajiya saboda hakan, Wanda ya azimci zamani (a here) to bai yi azimi ba, azimin kwana uku azimin zamani ne gaba ɗayansa", sai na ce: Lallai cewa ni zan iya sama da hakan, ya ce: "To ka yi azimin (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi -, ya kasance yana azimtar yini kuma ya sha yini, kuma ba ya gudu idan ya gamu da maƙiya".
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහල Kiswahili অসমীয়া Tiếng Việt ગુજરાતી Nederlands አማርኛ Azərbaycan മലയാളംالشرح
(Labari) ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana jeranta azimi ba ya ajiyewa tsawon shekara, kuma yana sallar dare gaba ɗayansa ba ya bacci, sai ya hana shi daga hakan, kuma ya ce masa: Ka yi azimi kuma ka huta, ka yi sallar dare kuma ka yi bacci. Kuma ya hane shi daga jeranta azimi da tsayuwar dare gaba ɗayansa, kuma ya ce masa: Lallai cewa kai idan ka aikata hakan idanka zai yi rauni saboda shi zai yi kogo zai shige, kuma zuciyarka zata gaji ta ƙosa saboda haka; babu azimi (ga) wanda ya azimci shekara; inda cewa shi bai samu ladan azimin ba dan saɓawa hani, kuma bai buɗe baki ba domin cewa shi ya kame. Sannan ya shiryar da shi zuwa azimin kwana uku a kowane wata shi ne azimin shekara; domin kowace rana (kwatankwacin ladan) kwanaki goma ne, kuma hakan shi ne mafi ƙarancin riɓanyawa ga kyakkyawa. Sai Abdullahi ya ce: Lallai ni zan iya sama da hakan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: To sai ka yi azimin (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi - shi ne mafificin azimi, ya kasance yana azimin yini kuma yana hutawa yini, kuma ya kasance ba ya gudu idan ya gamu da maƙiya; domin tsarin aziminsa ba ya raunana jikinsa ba.فوائد الحديث
Azimin kwana uku a kowane wata kamar azimin shekara ne gabaɗayanta, hakan domin kyakkywa ɗaya da kwatankwacin sa goma ne, sai ta zama kwana talatin, idan ya yi azimin kwana uku a kowane wata kamar shi ya azmici shekara ce gaba ɗayanta.
Daga usuluban kira zuwa ga Allah (akwai) kwaɗaitarwa a cikin aiki da ambatan ladansa da ladan dawwama a kansa.
AlKhaɗɗabi ya ce: A taƙaice ƙissar Abdullahi ɗan Amr cewa Allah - Maɗaukakin sarki - bai ɗorawa bawanSa ibadar azimi a keɓance ba, kai Ya bautar da shi da nau'ikan ibadu, da zai ƙarar da ƙoƙarinsa da ya taƙaita a waninsa, to abinda ya fi shi ne tattali a cikinsa dan sashin ƙarfinsa ya ragu ga waninsa, haƙiƙa an yi nuni zuwa ga hakan da faɗinsa - aminci ya tabbata agare shi - a (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi -: "Ya kasance ba ya gudu idan ya gamu da maƙiyi"; domin cewa shi ya kasance yana ƙarfafuwa da buɗa baki saboda yaƙi.
Hani daga zirfafawa da ɗorawa kai nauyi a cikin ibada, alheri shi ne lazimtar sunna.
Mazahabar Jumhur ɗin ma'abota ilimi ita ce karhancin azimin zamani (shekara a jere), kuma yana zama haram idan ya tsanantawa kansa kuma ya cutar da ita ya ɗora mata, ya kauce daga sunnar Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kuma ƙudirce cewa canja sunnarsa ya fi daga gareta.
التصنيفات
Azumin Taxawwu'i