Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah

Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai bayan (azimin) Ramadan, ita gwargwadan Sa'i ne (wanda) awonsa yakai mudun Nabiyyi huɗu. Mudun Nabiyyi: (Shi ne) cikin tafukan mutum madaidaici, na dabino ko alkama akan kowane musulmi; ɗa da bawa, namiji da mace, ƙarami da babba, hakan ga wanda a wajensa akwai abinda ya rage daga abin cin yininsa da darensa, (zai fitarwa) kansa da kuma wanda yake kula da su. Kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi.

فوائد الحديث

Zakkar fidda kai ta azimi tana wajaba a fitar wa yaro ita da babba, da ɗa da bawa, kuma ana yi wa waliyyin (yaro) da mamallakin (bawa) umarni da ita, kuma mutum yana fitarwa kansa da 'ya'yansa da wanda ciyarwarsu take wajaba akansa.

Zakkar fidda kai ba ta wajaba daga ɗan tayi, saidai an so (a fitar masa).

Bayanin abinda ake fitarwa a zakkar fidda kai, shi ne abincin mutane na al'ada.

Wajabcin fidda ita kafin sallar idi, abinda ya fi ta kasance a safiyar idi, kuma fitar da ita yana halatta kafin idi da kwana ɗaya ko kwanaki biyu.

التصنيفات

Zakkar Fidda Kai