إعدادات العرض
1- Babu komai na Zakka akan Musulmi cikin dokinsa
2- Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi*, kuma bamu gushe ba muna fitar da shi har saida Mu'awiya ɗan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi - ya gabato gurinmu yana mai aikin Hajji, ko yana mai Umarah sai ya yi wa mutane magana akan minbari, ya kasance daga abinda ya yi wa mutane magana da shi cewa ya ce: Lallai ni na ga cewa mudu biyu na alkamar Sham, sun yi daidai da sa'i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riko da hakan, Abu sa'id ya ce: Ammma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi, muddin dai na rayu har abada.
3- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.