إعدادات العرض
Wanda ya farar da (wani abu) daga al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa
Wanda ya farar da (wani abu) daga al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya farar da (wani abu) daga al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa". Daga Muslim: "Wanda ya aikata wani aiki wanda ba ya kan al'amarinmu to shi abin an mayar masa".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili فارسی မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá සිංහල தமிழ் ไทย دری Кыргызча or Kinyarwanda नेपाली Română Malagasy Lietuvių Oromoo Nederlands Soomaali Српски Українська ಕನ್ನಡ Wolof Mooreالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nuni akansa ba na Alkur’ani ko hadisi, to shi abin juyarwane akan mai shi ba abin karba ba ne a wurin Allah.فوائد الحديث
Ibadu an gina su ne akan abinda ya zone kawai a cikin Alkur’ani da sunna, ba zamu bautawa Allah - Madaukakin sarki - ba sai da abinda Ya shara'anta ba da bidi'o'i ko kirkirarrun abubuwa ba.
Addini ba ra'ayi ba ne, ko ganin kyan abu, kadai da bin Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Wannan hadisin dalili ne akan cikar Addini.
Bidi'a ita ce dukkanin abinda aka farar a Addini wanda babu shi a lokacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, da sahabbansa na akida ne ko magana ko aiki.
Wannan hadisin tushe ne daga tushen Musulunci, shi kamar ma'auni ne ga ayyuka, kamar yadda kowanne aikin da ba'a nufi zatin Allah - madaukakin sarki - da shi ba, to mai aikata shi ba shi da wani lada, hakanan kowanne aikin da bai zama ya dace da abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi ba to shi abin juyarwa ne akan mai aikata shi.
Fararrun abubuwan da aka hana su ne abinda suka kasance na al'amuran Addini, ba na duniya ba.
التصنيفات
Bidi'a