«Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku*, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».

«Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku*, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa da a ce ɗan Adam zai samu wani kwari cike da zinari, da zai so saboda kwaɗayinsa wanda shi ne ɗabi'arsa ta zama yana da wasu kwari biyun daban, kuma cewa shi ba zai gushe ba yana kwaɗayi akan duniya har sai ya mutu cikinsa ya cika da ƙasar ƙabarinsa.

فوائد الحديث

Tsananin kwaɗayin mutum akan tara dukiya da waninta na kayan jin daɗin rayuwar duniya.

Nawawi ya ce: A cikinsa akwai zargin kwaɗayi akan duniya da kuma son tara dukiya a cikinta da kuma kwaɗayinta.

Allah - Maɗaukakin sarki - Yana karɓar tuban wanda ya tuba daga siffofi ababan zargi.

Nawai ya ce: Hadisin ya zo ne akan hukuncin mafi yawancin mutane a kan kwaɗayin duniya, kuma faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba) yana ƙarfafarsa.

التصنيفات

Munanan Halaye, Zargin Son Duniya