Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne

Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya zagi ɗan uwansa musulmi, kuma hakan yana daga fasiƙanci shi ne fita daga yi wa Allah ɗa'a da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma yaƙar musulmi ga ɗan uwansa musulmi yana daga ayyukan kafirci, sai dai hakan kafirci ne ƙarami.

فوائد الحديث

Wajabcin girmama mutuncin musulmi da jininsa.

Girman lamarin zagin musulmi ba tare da wani haƙƙi ba; to mai zagin ba tare da wani haƙƙi ba fasiƙi ne.

Zagin musulmi da yaƙarsa yana raunana imani kuma yana tauye shi.

Sashin ayyuka ana ambatansu kafirci; koda basu kai ga kafirci babba mai fitarwa daga tafarkin Musulunci ba.

Abin nufi da kafirci a nan kafirci ƙarami wanda ba ya fitarwa daga Addini da haɗuwar Ahlus Sunnah; domin Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya tabbatar da 'yan uwantaka ta imani ga muminai a halin yaƙi tsakaninsu da kuma jayayyarsu, sai Allah Maɗaukakin sarki Ya ce; {Idan ƙungiyoyi biyu ta muminai suka yi faɗa to ku yi sulhu a tsakaninsu} zuwa faɗinSa; {Kaɗai muminai 'yan uwa ne}.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Munanan Halaye