Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai

Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce bai tashi daga gareta ba: «Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai» ta ce; Da badan haka ba da an bayyanar da ƙabarinsa, sai dai cewa an ji tsoron a riƙe shi a matsayin masallaci.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce ta tsananta gare shi kuma ya mutu a cikinta: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, Ya koresu daga rahamarSa; hakan domin cewa su sun riƙi ƙaburburan Annabawansu a matsayin masallatai. Ta hanyar yin gini a kansu ko yin sallah a wurinsu ko zuwa garesu (kallonsu). (Nana A'isha) Allah Ya yarda da ita ta ce: Da badan wannan hanin da gargaɗin daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tsoron sahabbai kan abinda za’a yi wa ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar yadda Yahudawa da Nasara suka yi wa ƙaburburan Annabwansu ba da anbayyanar da ƙabarinsa kuma an fito da shi.

فوائد الحديث

Wannan yana daga wasiyyoyinsa na ƙarshe daga abinda yake nuni akan muhimmancinsu da kuma kulawa da su.

Hani mai ƙarfi, da haramci mai tsanani daga riƙon ƙaburbura masallatai, da nufar yin sallah a wurinsu banda sallar jana'iza; to hakan hanya ce zuwa girmama mamacin da kuma ɗawafi a ƙabarinsa da shafa ƙinshiƙansa da kiran sunansa, kuma dukkanin wannan yana daga shirka da kuma hanyoyinta.

Tsananin himmatuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kulawarsa a kan Tauhidi, da kuma tsoronsa daga girmama ƙaburbura; domin hakan yana kai wa zuwa ga shirka.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kiyaye Annabinsa - tsira da amincin su tabbata agare shi - da ayi shirka a wurin ƙabarinsa, sai ya cusawa sahabbansa da waɗanda ke bayansu su kiyaye ƙabarinsa da kada a fito da shi.

Aikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - da wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kwaɗayinsu akan Tauhidi.

Hani daga kamanceceniya da Yahudawa da Nasara, da kuma gini akan ƙaburbura yana daga al'adunsu.

Daga cikin riƙon kaburbura masallatai akwai yin sallah a wurinsu, da kuma zuwa garesu (wato kallonsu), ko da ba a gina masallaci ba.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya, Ziyarar Makabarta