Hakika na fadi wasu Kalmomi Hudu bayanki da za'a aunasu da abinda kika fada a wunin da sun rinjayesu: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiya gare shi, yawan Halittar sa, da yardar kansa, da ma'aunin Al-arshinsa, da Rubutun Kalmominsa.

Hakika na fadi wasu Kalmomi Hudu bayanki da za'a aunasu da abinda kika fada a wunin da sun rinjayesu: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiya gare shi, yawan Halittar sa, da yardar kansa, da ma'aunin Al-arshinsa, da Rubutun Kalmominsa.

An rawaito daga Juwairiyya 'yar Haris -Allah yarda da ita- ta ce: Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gae shi ya ce da ni: "Hakika na fadi wasu Kalmomi Hudu bayanki da za'a aunasu da abinda kika fada a wunin da sun rinjayesu: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiya gare shi, yawan Halittar sa, da yardar kansa, da ma'aunin Al-arshinsa, da Rubutun Kalmominsa."

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Juwairiyya -Allah ya kara mata yarda- tana bada Labari cewa Annabi ya futo daga wurinta a lokacin Sallar Asuba sannan ya dawo lokacin Walaha, sai ya sameta tana ta anbaton Allah Madaukaki sai ya bata labarin cewa ya fadi wasu kalmomi hudu bayanta da za'a hada su da abunda ta fada zai daidai da su a lada, koma ya rinjaye ta a Ma'aunin aiki sannan ya bayyana su da fadinsa: "Tsarki ya tabbata ga Allah da godiya gare shi, yawan Halittar sa, da yardar kansa, da ma'aunin Al-arshinsa, da Rubutun Kalmominsa." ai Tasbihi mai yawa wanda zai kai yawan halittarsa, kuma babu wanda yasan yawansu sai Allah, kuma Tasbihi wanda zai kai girman yardarsa Madaukaki, kuma Tasbihi wanda yakai nautin Al-arshi da ace za'a iya taba shi, Tasbihi wanda zai ta ci gaba har abada ba zai Kare ba.

التصنيفات

Zikirin Safiya da Maraice