إعدادات العرض
Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa
Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa
Daga Bahzu ɗan Hakim daga babansa daga kakansa ya ce: Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa».
[Hasan ne]
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو हिन्दी 中文 Kurdî Português Tiếng Việt অসমীয়া Nederlands Kiswahili አማርኛ ગુજરાતી සිංහල ไทยالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mafi cancantar mutane da yi wa biyayya, da kyautata masa, da kyakkyawar mu'amala, da tsaftatacciyar mu'amala, da abokantakarsa da sadar da zumuncinsa: Ita ce uwa, kuma ya ƙarfafa haƙƙin uwa akan waninta da maimaitawarsa sau uku; dan bayanin falalarta akan ragowar mutane ba tare da togancewa ba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai bayyana wanda yake biye mata a biyayya: Sannan uba, sannan mafi kusanci sai mafi kusanci daga 'yan dangi, kuma a duk lokacin da ya zama ya fi kusanci to ya zama mafi cancanta da sadar da zumunci daga mafi nesa.فوائد الحديث
A cikin hadisin akwai gabatar da uwa, sannan uba, sannan mafi kusanci sai mafi kusanci, gwarwadan darajojinsu a kusanci.
Bayanin matsayin mahaifa musamman uwa.
A cikin hadisin ya maimaita yi wa uwa biyayya sau uku; hakan dan girman falalarta akan 'ya'yanta, da kuma yawan abinda take ɗauka na wahalhalu da gajiya da kuma wahalar ciki, sannan haihuwa, sannan shayarwa, abubwan da uwa take kaɗaitaka da shi, sannan ta yi tarayya da uba a cikin tarbiyya.
التصنيفات
Falalar bin Iyaye