إعدادات العرض
Kwatankwacin muminin da yake karanta AlKur'ani kamar gawasa ne, kanshinta mai dadi ne, kuma dandanonta mai dadi ne, kuma kwatankwacin muminin da ba ya karanta AlKur'ani kamar dabino ne ba shi da kanshi amma dandanonsa ma zaki ne
Kwatankwacin muminin da yake karanta AlKur'ani kamar gawasa ne, kanshinta mai dadi ne, kuma dandanonta mai dadi ne, kuma kwatankwacin muminin da ba ya karanta AlKur'ani kamar dabino ne ba shi da kanshi amma dandanonsa ma zaki ne
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminin da yake karanta AlKur'ani kamar gawasa ne, kanshinta mai dadi ne, kuma dandanonta mai dadi ne, kuma kwatankwacin muminin da ba ya karanta AlKur'ani kamar dabino ne ba shi da kanshi amma dandanonsa ma zaki ne, kuma kwatankwacin munafikin da yake karanta AlKurani kamar nana ne kanshinsa mai dadi ne amma dandanonta mai daci ne, kuma kwatankawacin munafikin da ba ya karanta AlKura'ni kwatankwacin guna ce ba ta da kanshi, kuma dandanonta mai daci ne".
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी Español Kurdî Português සිංහල Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá ئۇيغۇرچە Tiếng Việt Kiswahili پښتو অসমীয়া دری Кыргызча or Malagasy Čeština नेपाली Oromoo Română Nederlands Soomaali తెలుగు മലയാളം Српски ไทย Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Lietuviųالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana karkasuwar mutane a karatun AlKur'ani da amfanuwa da shi: Kashi na farko: Muminin da yake karanta AlKur'ani kuma yake amfanuwa da shi, to shi kamar gawasa ne, mai dadin dandano da kanshi, da kyakkyawan launi, kuma amfaninsa mai yawa ne, shi yana aiki da abinda ya karanta, kuma yana amfanar bayin Allah. Kashi na biyu: Muminin da ba ya karanta AlKur'ani, to shi kamar dabino ne, dandanonsa mai zaki ne, kuma ba shi da kanshi, to zuciyarsa mai tattare da imani ce kamar tattarowar dabino akan zaki a dandanonsa da cikinsa, da rashin bayyanar kanshi gare shi wanda mutane za su shaka; Saboda rashin bayyanar karatu daga gare shi wanda mutane za su ji dadin jinsa. Na uku: Munafikin da yake karanta AlKur'ani: To shi kamar nana ne, tana da dadin kanshi kuma dandanonta mai daci ne, ta inda bai gyara zuciyarsa da imani ba, kuma bai yi aiki da AlKur'ani ba, kuma yana bayyana ga mutane cewa shi muminine, to kanshinta mai dadi yana kama da karatunsa, dandanonta mai daci kuma yana kama da kafircinsa. Na hudu: Munafikin da ba ya karanta AlKur'ani, to shi kamar guna ne, ta inda ita ba ta da kanshi, da kuma dacin dandanonta, to rashin kanshinta ya yi kama da rashin kanshinsa; Saboda rashin karatunsa, kuma dacin dandanonta ya yi kama da dacin kafircinsa, cikinsa ya kadaita daga imani, zahirinsa kuma babu amfani a cikinsa, kai shi mai cutarwa ne.فوائد الحديث
Bayanin falalar mai dauke da AlKur'ani mai aiki da shi.
Daga hanyoyin koyarwa akwai buga misalai; Dan kusanto da fahimta.
Yana kamata ga musulmi ya zama yana da wani wuridai da yake yi kullum na karatun littafin Allah - Madaukakin sarki -.
التصنيفات
Falalar Kulawa da Al-qur’ani