Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa

Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wajibi ne mai ƙarfi a kan kowanne musulmi baligi mai hankali ya yi wanka a kowanne kwana bakwai daga sati rana ɗaya, sai ya wanke kansa da jikinsa a wannan ranar; don neman tsarki da tsafta, mafi cancantar waɗannan kwanukan (ita ce) ranar Juma'a, kamar yadda aka fahimta daga sashin riwayoyi, wanka ranar Juma'a kafin sallah mustahabbi ne mai ƙarfi, ko da ya yi wanka ranar Alhamis misali, abinda ya cire shi daga wajabcin (shi ne) faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -: "Mutane sun kasance suna wa kawunansu hidima, sun kasance idan sun tafi zuwa Juma'a sai su tafi a yanayinsu: sai aka ce da su: Ina ma dai kun yi wanka". Bukhari ne ya ruwaito shi, a cikin wata riwayar ta shi: "A tare da su akwai wari" wato warin gumi da makamanncin hakan, a tare da hakan aka ce da su: Ina ma dai kun yi wanka

فوائد الحديث

Damuwa da kulawar musulunci game da tsafta da kuma tsarki.

Wankan Juma'a mustahabbi ne mai ƙarfi don yin sallah.

Ambaton kai ko da ambaton jiki ya tattaroshi; don ba shi muhimmanci ne.

Wanka yana wajaba a kan duk wanda aka samu a tare da shi akwai wari abin ƙi wanda mutane suke cutuwa da shi.

Mafi ƙarfin yini don yin wanka (shi ne) ranar Juma'a don falalarta

التصنيفات

Wanka