Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala

Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Mun dawo tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Makka zuwa Madina har sai da muka kasance a wani ruwa a hanya, sai wasu mutane suka yi gaggawar (sallar) La'asar, sai suka yi alwala alhali suna gaggawa, sai muka kai gare su alhali karshen kafafuwanusu suna haske (lam’a) ruwa bai tabasu ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tafiya daga Makka zuwa Madina a tare da shi akwai sahabbansa, sai suka samu ruwa a hanyarsu, sai wasu daga sahabbai suka yi gaggawar alwala dan sallar La'asar har karshen kafafuwansu suka dinga bayyana ga mai kallo saboda bushewarsu daga ruwa, sai Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Azaba da halaka a cikin Wuta sun tabbata ga masu takaitawa a wanke karshen kafa a lokacin alwala, kuma ya umarcesu da sukai matuka a cikin cika alwala.

فوائد الحديث

Wajabcin wanke kafafuwa a alwala; domin da shafa ya halatta da wanda ya bar wanke karshen kafa ba'a yi masa narko da wuta ba.

Wajabcin game dukkan gabban da ake wankewa da wankewa da ruwa, kuma wanda ya bar wani sashi karami daga abinda ya wajaba a wanke shi da gangan da kuma sakaci to sallarsa ba ta inganta ba.

Muhimmancin ilimantar da jahili da kuma shiryar da shi.

Malami ya yi inkarin abinda yake gani na tozartar da farillai da sunnoni ta hanyar da ta dace.

Muhammad Ishak al-Dahlawi ya ce: Cika (alwala) nau'i uku ne: Farilla shi ne game gaba da (ruwa) sau ɗaya, da sunna shi ne wankewa sau uku, da kuma mustahabbi shi ne tsawaitawa tare da wankewa sau uku.

التصنيفات

Sifar Al-wala