إعدادات العرض
Mai kira zai kira: Lallai cewa ku zaki yi lafiya ba za ku yi masassara ba har abada, kuma ku zaku rayu ba za ku mutu ba har abada, kuma cewa ku zaku samartaku ba zaku tsufaba har abada, kuma cewa ku zaku ni'imtu ba zaku yanke ƙauna ba har abada'
Mai kira zai kira: Lallai cewa ku zaki yi lafiya ba za ku yi masassara ba har abada, kuma ku zaku rayu ba za ku mutu ba har abada, kuma cewa ku zaku samartaku ba zaku tsufaba har abada, kuma cewa ku zaku ni'imtu ba zaku yanke ƙauna ba har abada'
Daga Abu Sa'id al-Khudri da Abu Hurarira - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai kira zai kira: Lallai cewa ku zaki yi lafiya ba za ku yi masassara ba har abada, kuma ku zaku rayu ba za ku mutu ba har abada, kuma cewa ku zaku samartaku ba zaku tsufaba har abada, kuma cewa ku zaku ni'imtu ba zaku yanke ƙauna ba har abada' wannan faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -: {Sai a yi kira cewa wancananku aljanna an gadar muku da ita saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa} [al-A'araf: 43].
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහල Nederlands অসমীয়া Kiswahili ગુજરાતી አማርኛ پښتو ไทย Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa mai kira zai kira 'yan aljanna alhali su suna cikinta suna ni'imtuwa: Lallai cewa ku zaku samu lafiya ba zaku yi masassara a cikin aljanna ba har abada duk yadda ƙarancin masassarar take, kuma cewa ku zaku rayu ba zaku mutu a cikinta ba har abada koda ya kasance bacci ne wanda shi ne mutuwa ƙarama, kuma cewa ku zaku zama samari a cikinta ba zaku tsufa a cikinta ba har abada, kuma cewa ku zaku ni'imtu ba zaku yi baƙin ciki ba ko ku yanke ƙauna a cikinta ba har abada, hakan (shi ne) faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -: {Sai a yi kira cewa wancananku aljanna an gadar muku ita saboda a binda kuka kasance kuna aikatawa} [al-A'araf: 43].فوائد الحديث
Mafi girman ƙuncin ni'imar rayuwar duniya duk yadda mai ita yakai na wadata abubuwa ne huɗu:
Masassara, da mutuwa, da tsufa, da yanke ƙauna da baƙin ciki saboda tsoro daga maƙiyi da talauci da yaƙi da wanin hakan, 'yan aljanna sun kuɓuta daga gare su, sai ni'ima mafi cika ta tabbata ga 'yan aljanna.
Saɓawar ni'imar aljanna daga abinda ke cikin duniya na ni'ima; domin cewa ni'imar aljanna babu tsoro a cikinta, amma ni'imar duniya ba ta dawwama kuma raɗaɗi da masassara su ne ke zuwa mata.
Kwaɗaitarwa a cikin aiki na gari wanda za'a sadu da shi zuwa ni'imar aljanna.
التصنيفات
Sifar Al-janna da Wuta