إعدادات العرض
Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in ya samu
Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in ya samu
Daga Amr Dan Sulaim Al-Ansari ya ce: Na shaida Abu sa'id ya ce: Na shaida Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in ya samu".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Português සිංහල Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá ئۇيغۇرچە Tiếng Việt Kiswahili پښتو অসমীয়া دری Malagasy or Čeština नेपाली Oromoo Română Nederlands Soomaali తెలుగు ไทย മലയാളം Кыргызча Српски Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Lietuvių Wolof Magyar ქართული Mooreالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanka ranar Juma'a abu ne mai karfi kamar wajibi a hakkin kowanne namiji baligi daga musulmai daga wanda juma'a ta wajaba akansa, kuma ya tsaftace hakoransa da asuwaki da makancinsa, ya kuma shafa tirare da kowanne irin tirare mai kanshi.فوائد الحديث
Karfafar mustahabbancin wanka ranar Juma'a akan kowanne mutum musulmi baligi.
Tsafta da kawar da wari mara kyau abin nema ne a shari'a ga kowanne musulmi.
Girmama ranar Juma'a, da yin tanadi saboda ita.
Karfafa mustahabbancin asuwaki a Juma'a.
Anso Shafa tirare da kowanne irin tirare mai ƙanshi kafin tafiya Juma'a.
Mace idan ta fita daga gidanta dan sallah ko waninta, to tirare ba ya halatta gareta; Dan nunin sunna akan haramcin hakan.
Wanda ya isa mafarki shi ne baligi, balaga tana faruwa ne da wasu alamomi.
Uku daga ciki mace da namiji suna tarayya a cikinsu, su ne:
Na farko: Cikar shekara goma sha biyar.
Na biyu: Idan gashi mai kauri ya tsiro a gefen farji.
Na uku: Zubar maniyyi ta hanyar mafarki ko ta hanyar sha'awa koda ba tare da mafarki ba.
Amma alama ta hudu to ita ce take kebantar mace, ita ce kuwa: Al’ada, idan mace ta yi al’ada to ta zama baliga.
التصنيفات
Hukunce Hukuncen Sallar Jumu'a