Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi

Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi

Daga Umar ɗan khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da wani mutum ya ɓullo mana mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba a ganin gurbin tafiya a gareshi, kuma wani daga cikinmu bai sanshi ba, har ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya jingina gwiwoyinsa zuwa gwiwoyinsa, ya ɗora tafukansa a kan cinyoyinsa, sai ya ce: Ya Muhammad, ba ni labari game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi" ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Sai muka yi mamakinsa, yana tambayarsa yana gasgatashi, ya ce: Ka ba ni labari game da imani, ya ce: "Ka ba da gaskiya da Allah, da mala'ikunsa, da littattafansa, da manzanninsa, da ranar lahira, ka ba da gaskiya da kaddara alherinta da sharrinta" ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: ka ba ni labari game da kyautayi, ya ce: "Ka bautawa Allah kamar kai kana ganinsa, idan ka kasance ba ka ganinsa, to, shi yana ganinka" Ya ce: ka ba ni labari game da al-ƙiyama, ya ce: Wanda ake tambayar bai fi wanda yake tambayar sani ba". Ya ce: Ka ba ni labarin alamominta, ya ce: "Kuyanga za ta haifi uwargijiyarta, kuma za ka ga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi suna gasar tsawaita gidaje" Ya ce: Sannan ya tafi, sai na zauna ɗan wani lokaci sannan ya ce da ni: "Ya Umar, shin ka san waye mai tambayar?" Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "To, lallai Jibrilu ne ya zo muku don ya sanar da ku addininku".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - yana ba da labari cewa Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya fito wurin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a surar wani mutum namiji ba a sanshi ba, daga siffofinsa cewa tufafinsa masu tsananin fari ne, gashin kansa kuma mai tsananin baƙi ne, ba a ganin gurbin tafiya a gareshi na bayyanar gajiya, da ƙura, da rarrabewar gashi, da dattin tufafi, kuma wani ɗaya daga mahalartan bai sanshi ba, alhali su suna zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - irin zaman mai neman sani, sai ya tambayeshi game da musulunci, sai ya ba shi amsa da waɗannan rukunan, waɗanda suka ƙunshi iƙirari da shaida biyu, da kiyayewa a kan salloli biyar, da ba da zakka ga waɗanda suka cancanta, da azimin watan Ramadan, da ba da farillar Hajji a kan mai iko. Sai mai tambayar ya ce: Ka yi gaskiya, sai sahabbai suka yi mamaki daga tambayarsa mai nuni a kan rashin saninsa a cikin abin da yake bayyana da kuma gasgatashi. Sannan ya tambayeshi game da imani, sai ya amsa masa da waɗannan rukunan guda shida masu ƙunshe da imani da samuwar Allah - Maɗaukakin sarki - da siffofinsa, da kaɗaitashi da ayyukansa kamar halitta, da kaɗaitashi da ibada, kuma cewa mala'iku waɗanda Allah Ya haliccesu daga haske bayi ne ababen girmamawa ba sa saɓawa Allah - Maɗaukakin sarki - kuma suna aiki da umarninsa, da yin imani da littattafan da aka saukar ga manzanni daga Allah - maɗaukakin sarki -, kamar Al-ƙur'ani da At-Taura da Injila da wasunsu, da kuma (imani) da manzanni masu isar da Addinin Allah, daga cikinsu akwai Nuhu, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da na ƙarshensu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -, da wasunsu daga Annabawa da manzanni, da imani da ranar lahira, abin da ke bayan mutuwa yana shiga cikinsu na kabari da rayuwar barzahu, kuma cewa mutum za a tasheshi bayan mutuwa kuma za a yi masa hisabi, kuma makomarsa za ta zama ko dai zuwa aljanna ko zuwa wuta, da imani da cewa Allah Ya ƙaddara abubuwa gwargwadon yadda iliminsa ya rigaya da shi, kuma hikimarsa ta hukuntashi da rubutunsa ga hakan, da mashi'arsa gareshi, da afkuwarsu gwargwadon yadda ya ƙaddarasu, ya kuma haliccesu don haka. Sannan ya tambayeshi game da kyautatawa, sai ya ba shi labari da cewa kyautatawa ita ce ya bautawa Allah kamar shi yana ganinsa, idan bai samu damar kaiwa zuwa wannan matsayin ba, to, ya bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - kamar Allah Yana ganinisa, na farko shi ne matsayin Mushahada, ita ce mafi ɗaukaka, na biyu shi ne matsayin Muraƙabah. Sannan ya tambayeshi yaushe ne al-ƙiyama? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa sanin al-ƙiyama yana daga abin da Allah Ya keɓanta da saninsa, babu wani daga halitta da ya sanshi, wanda ake tambayar da mai tambayar. Sannan ya tambayeshi game da alamomin al-ƙiyama? Sai ya bayyana masa cewa daga alamominta akwai yawan kuyangi (sa-ɗaka) da 'ya'yansu, ko yawan saɓawar 'ya'ya ga iyayensu, mata za su dinga yi musu mu'amala irirn mu'amalar bayi, kuma cewa makiyaya dabbobi da talakawa za a shinfiɗa musu duniya a ƙarshen zamani, sai su dinga alfahari a ƙawata gine-gine da ɗaukakasu. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labari da cewa mai tambayar shi ne Jibrilu ya zo don sanar da sahabbai wannan addinin miƙaƙƙe.

فوائد الحديث

Kyawawan ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma yana zama tare da sahabbansa su ma suna zama a wurinsa.

Halaccin tausasawa ga mai tambaya da kusanto da shi, don ya samu damar tambaya ba tare da takura ko tsoro ba.

Ladabi tare da malami kamar yadda Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya yi, yayin da ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - irin zaman mai ladabi don ya karɓa daga gareshi.

Rukunan musulumci guda biyar ne, kuma rukunan imani guda shida ne.

Yayin haɗuwar musulunci da imani ana fassara musulunci da al'amura na zahiri, imani kuma da al'amura na baɗini.

Bayanin cewa addini darajoji ne mabanbanta, daraja ta farko: Musulunci, ta biyu: Imani, ta uku: Kyautatawa, ita ce ƙololuwarsu.

Asali ga mai tambaya shi ne rashin ilimi, jahilci shi ne mai sa tambaya, saboda haka sahabbai suka yi mamaki game da tambayarsa da gasgatawarsa.

Farawa da mafi muhimmanci sannan mai bi masa; domin an fara da shahada biyu wajen fassara musulunci, kuma anfara da imani da Allah a fassarar imani.

Tambayar ma'abota ilimi abin da mai tambaya bai jahilceshi ba, don ya sanar da waninsa.

Sanin al-ƙiyama yana daga abin da Allah Ya keɓanta da saninsa.

التصنيفات

Aqida