إعدادات العرض
Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah
Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah
Daga Abdullahi ɗan Busr - Allah Ya yarda da shi - cewa wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah lallai shari'un musulunci haƙiƙa sun yi mini yawa, ka sanar dani wani abu wanda zan rataya da shi, sai ya ce: "Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Português සිංහල Nederlands অসমীয়া Tiếng Việt Kiswahili ગુજરાતી پښتو Oromoo አማርኛ ไทย Română മലയാളംالشرح
Wani mutum ya kai ƙara wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa nafilifilin ibadu sun yi masa yawa har ya gajiya daga yin su saboda rauninsa, sannan ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi ga wani aiki mai sauki mai jawo lada mai yawa wanda zai rataya da shi ya yi riƙo da shi. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nunar masa harshensa ya zama ɗanye mai motsawa saboda dawwamar ambatan Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - a kowane lokaci da hali; na tasbihi da tahmidi da istigafari da addu'a da makamancin hakan.فوائد الحديث
Falalar dawwama akan ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
Daga girman falalar Allah (akwai) sawwaƙe sabubban lada.
Fifikon bayi a rabonsu daga ƙofofin aikin lada da alheri.
Yawan ambatan Allah da harshe tasbihi da tahmidi da hailala da kabbara da wanin hakan tare da dacewar zuciya yana tsayawa matsayin yawa da yawan nafilifilin ayyukan ɗa'a.
Lurarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga masu tambaya da amsawa kowa da abinda ya dace da shi.
التصنيفات
Falalar Zikiri