Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa

Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga abubuwa huɗu: Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa) ta Addini da duniya kuma in tabbata akan Musulunci, in nisanci faɗawa cikin saɓon da yake gusar da ni'imomi. Na biyu: (Da juyawar lafiyarKa) da canjata zuwa bala'i; to ina roƙonKa dawwamar lafiya, da kuɓuta daga radaɗi da cututtuka. Na uku: (Da shammatar azabarKa) daga bala'i ko saɓo, azaba da uƙuba idan suka zo fuj'a bagtatan, to babu wani lokaci a wannan dan tuba da riska, wanda aka shafa da su zai zama mafi girma kuma mafi tsanani. Na huɗu: (Da dukkan fushinKa) da sabubban da suke wajabta fushinKa; domin wanda Ka yi fushi da shi to haƙiƙa ya taɓe kuma ya yi asara. Haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zo da lafazin jam'i; dan ya ƙunshi sabubban fushinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - daga maganganu da ayyuka da ƙudirce-ƙudierce.

فوائد الحديث

Buƙatuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -.

Waɗannan neman tsarin masu albarka sun ƙunshi: Dacewa ga godewar ni'imomi, da kiyayewa daga afkawa cikin saɓo; domin cewa su suna gusar da ni'imomi.

Kwaɗayi daga barin nisanta daga guraren fushin Allah - Maɗaukakin sarki -.

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga shammatar azabar Allah - Maɗaukakin sarki -; domin cewa Shi idan Ya yi wa bawa azaba to haƙiƙa Ya saukar masa da bala'in da ba zai iya tunkuɗeshi ba, kuma ba zai nemi kariyar ragowar halittu ba, koda sun taru gaba ɗaya.

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nemi tsari daga juyawar lafiyarSa - tsarki ya tabbatar maSa -; domin cewa shi idan Allah ya kasance ya keɓance shi da lafiyarSa to haƙiƙa ya rabauta da alherin duniya da lahira, idan ta juya daga gare shi to haƙiƙa an taɓa shi da sharrin duniya da lahira, domin cewa lafiya da ita ce gyaruwar Addini da duniya (suke).

التصنيفات

Addu’o’I da aka samu daga Annabi