Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta

Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita addu'a da addu'a gamammiya, daga cikinsu: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma Ka tsaremu azabar wuta", Ita ta tattaro kyau a duniya na arziki mai dadi, mayalwaci na halal, da mace ta gari, da da wanda ido zai yi farin ciki da shi, da hutu, da ilimi mai amfani, da makamancin hakan na abububuwan da ake so na halal, kyakkyawa a lahira na kubuta daga ukubobin kabari da tsayuwa da wuta, da samuwar yardar Allah, da rabauta da ni'ima madawwamiya, da kusanci ga Ubangiji Mai jin kai a lahira.

فوائد الحديث

An so addu'a da addu'o'i masu tattarowa, dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Mafi cika mutum ya hada tsakanin alherin duniya da lahira a addu'arsa.

التصنيفات

Addu’o’I da aka samu daga Annabi